1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmaki kan sansanin Alƙa'ida a Mali

September 19, 2010

Ana ci gaba da kaiwa sansanonin ƙungiyar Alƙa'ida dake arewacin Afirka hari, inda dakarun Moritaniya ke jagorantar farmakin

https://p.dw.com/p/PG6N
Sojojin Moritaniya dake yaƙi da Alƙa'idaHoto: Mohamed Mahmoud Aboumaaly

A rana ta uku, sojojin ƙasar Moritaniya sun ci gaba da yin luguden wuta kan sansanonin ƙungiyar Alƙa'ida dake kusa da iyakarsu da ƙasar Mali, inda aka hallaka 'yan ƙungiyar masu yawa. Dakarun Moriteniyan dai da fari sun kai farmaki da motocin suke amma da abun ya yi ƙamari sun fara amfani da jiragen yaƙi.

Ƙasar Faransa wanda ta yi wa ƙasashen yakin wato Mali, Aljeriya, Nijar da ita kanta Moritaniya mulkin mallaka tace babu dangantakan a farmakin sojin Moriteniya da sace baƙin da ake zargin Alƙa'ida ta yi a jamhuriyar Nijar a wannan makwan. Farmakin ya nuna ýadda Alƙa'ida ke ƙara bazuwa a yankin arewacin Afirka.

Farmakin na sojojin Moritaniya ya zo ne a dai-dai lokacin da ake zargin ƙungiyar ta Alƙa'ida da sace wasu ma'aikatan baƙi Faransawa biyar da ɗaya ɗan ƙasar Togo da Madagaska a cikin jamhuriyar Nijar. Wani kakakin sojojin Mauritaniya ya ce dakarunsu tun a jiya sun hallaka 'yan Alƙa'ida 12 a wani gumurzu da aka yi, kana suma sojojin sun rasa mutane biyu.

Tun a shekaran jiya dai jami'an tsaron ƙasar Aljeriya su ka ce ana wata fafatawa tsakanin sojin Mauritaniya da 'yan tsagerun Alƙa'ida da ke arewacin Afirka.

Dakarun Moritaniya cikin motoci kimanin 20 su ka shiga faɗan a kilomita 100 daga birnin Timbuktu na ƙasar Mali. Ba'a dai bayyana cewa ko wannan karawa ta na alaƙa da sace turawan Faransa da aka yi a jamhuriyar Nijar ba. Jami'an tsaron Aljeriya suka ce waɗanda suka sace mutanen a yankin Arlit dake jamhuriyar Nijar, sun tsallaka da su cikin hamadar ƙasar Mali.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu