1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin farmakin sojojin Najeriya gida jarida

Uwais Abubakar Idris SB
January 7, 2019

Martani game da mamayen da sojoji suka yi a kan ofishin jaridar Daily Trust da ke Maiduguri da Abuja da Lagos, inda suka kwashe naurorin komfutoci da ma kame wasu 'yan jaridu bisa wani labara da jaridar ta wallafa.

https://p.dw.com/p/3B8j5
Reporter ohne Grenzen Logo
Hoto: Getty Images/AFP/B. Guay

A cikin shiri da ke nuna yanayi na harzuka ne sojojin suka afka ofishin na kamfanin jaridar Daily Trust da ke Abuja tare da korari duk ma'aikatan da ke ciki da kuma kwasar naurorin komputoci, lamarin da ya harzuka mutanen da dama a ciki da wajen Najeriya saboda kalon da fahimtar da ake masa a matsayin wani sabon kokari na rufe bakin ‘yan jaridu da yi wa ‘yancin fadin albarkacin baki hawan kawara a kasar, wacce ke tinkaho da bin tafarki na mulkin dimukuradiyya.

Kan labarin da jaridar ta wallafa da ya bayyana shirin da sojojin ke yi na kai harin sake kwace Baga da ma wasu garuruwan da ake ikirarin sun subuce daga sojojin Najeriya da ma fusata sojojin da suka dauki wannan mataki, suna ikirarin cewa an tona asirinsu na shirin kai farmaki na yaki da suka ce ya saba sashi na 1 da na 2 na dokar bayanan sirri ta Najeriya, To sai dai ga Mallam Shuaibu Leman sakataren kungiyar ‘yan jaridun Najeriya ya ce wannan ba dalili ne da za su amince da shi ba.

Medienfreiheit
Hoto: Imago/Martin Bäuml Fotodesign

Tuni kungiyar kwadagon Najeriya ta bi sahun al'ummar kasar da ke yin tir da matajin da sojojin suka dauka. Comrade Nasiru Kabir shine kakakin kungiyar kwadago ta ULC.

Hukumomin sojojin Najeriya sun fitar da sanarwa wacce Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya sanya hannu suna cewa sun je kai takardar samace ne ga ‘yan jaridun da suke zargi a yanayi da ya bai wa kowa mamaki domin motoci ne cike da sojoji suka afka a kamfanin jaridar.

A yayin da sanya bakin da fadar shugaban Najeriya ta sanya sojojin suka janye za a sa ido a ga irin sasantawar da suke son a yi a wannan lamari da a fili ya keta hadin ‘yacin aikin jarida a Najeriya.