1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar bututun man fetir a Nijeriya

May 12, 2006
https://p.dw.com/p/Buyd
Mutane kimanin 150 zuwa 200 suka rasa rayukansu a fashewar wani bututun mai a kusa da Legas cibiyar hadahadar kasuwanci a tarayyar Nijeriya. Rahotanni sun nunar da cewa har yanzu akwai gawawwakin mutane da suka kone kurmus a wurin da bututun yayi bindiga. Rahotannin farko sun ce bututun ya kama da wuta ne bayan da wasu bata gari dake satar man fetir suka lalata bututun a yankin Ilado dake wajen birnin na Legas. Sau da yawa dai talakawa a Nijeriya kasar da tafi arzikin man fetir a nahiyar Afirka, kan lalata bututun mai don samun man girki ko kuma sayarwa a kasuwannin bayan fage. A cikinw atan satumban shekara ta 2004 mutane 50 suka rasu a fashewar wani bututun mai a kusa da birnin na Legas.