1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan warware rikicin gabas ta tsakiya

July 31, 2013

Amurka na fatan ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Izraela da Palastinu nan da watanni 9 masu zuwa. Sai dai ta ce hakan fata ne amma ba wa'adi ba.

https://p.dw.com/p/19HwQ
Von rechts: Die israelische Justizministerin Tzipi Livni, US-Außenminister John Kerry und Israels Ministerpräsident Benjamin Netanjahu am 23. Mai 2013 in Jerusalem (Foto: Getty Images) US State of Secretary John Kerry stands with Israeli Defence Minister Boogie Yaalon (L), Minister of International Relations Yuval Steinitz (2L), Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu (C) and Minister of Justice Tzipi Livni (R), at Netanyahu's office on May 23, 2013 in Jerusalem, Israel. (Photo by Uriel Sinai/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Wani Jami'in diplomasiyyar a birnin kudus din kasar Isra'ila ya bayyana cewar, cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinu cikin watanni tara, fata ne kawai amma ba wa'adi ba. Babban jami'i a ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus Michael Ratney, ya fada wa taron manema labaru cewar, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai rika ziyartar yankin akai-akai, domin ganin yadda shirin neman zaman lafiyar ke tafiya. Ya kara da cewar wani Janar na Amurka mai ritaya John Allen, zai yi aiki kafada da kafada da bangarorin biyu a kan batutuwan tsaro. A wannan mako ne dai aka kaddamar da sabuwar tattaunawa tsakanin Isra'ila da Palastinu, bayan rushewar da yayi tun shekaru biyar da suka gabata. Kerry ya nunar da cewar, akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu nan da watanni tara masu zuwa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Muhammad Nasir Awal