1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Bangui bayan zabe

Yusuf BalaFebruary 15, 2016

Kujeru 105 ne dai na majalisar 'yan takara 1,800 suka fafata a kansu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1HvRE
Zentralafrikanische Republik Bangui Wahlen Wahllokal
Jami'ar zabe bayan kammala kada kuri'aHoto: picture-alliance/AP Photo/H. Diaspora

Jami'an zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun fara kirga kuri'un zaben da aka kada a ranar Lahadi bayan tsawon lokaci ana dakon wannan rana kafin zabukan 'yan majalisa da zagaye na biyu a zaben shugaban kasa, abin da akewa fatan zai yi sanadi na samun zaman lafiya bayan lokaci mai tsawo ana fama da fadace-fadace mai nasaba da banbancin addini da ma kabila a kasar wacce ta samu 'yanci a shekarar 1960.

An dai kai ga kammala zaben lafiya bisa tsauraran matakai na tsaro bayan da jami'an kwantar da tarzoma na Majalisar Dinkin Duniya suka bazu a sassa daban-daban na kasar.

Anicent Georges Dologuele tsohon ma'aikacin banki dan shekaru 58 ya samu sama da kashi 23 cikin dari na kuri'un da ka kada, yayin da abokin takararsa da ya zo na biyu Faustin Archange Toudera farfesan lissafi shi ma dan shekaru 58 ya samu sama da kashi 19 cikin dari a zagayen farko na zaben.

Al'ummar wannan kasa dai sun sake zaben 'yan majalisa da aka soke zabensu saboda kura-kurai a zaben na 30 ga watan Disambar bara, Kujeru 105 ne dai na majalisar 'yan takara 1,800 suka fita a ka fafata dan kaiwa garesu.