1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ficewar Birtaniya daga EU zai janyo karin haraji

Mohammad Nasiru AwalJune 15, 2016

Sakataren kudin Birtaniya ya yi gargadi game da karin haraji idan kasar ta fice daga kungiyar EU a kuri'ar raba gardama ta ranar 23 ga watan Yuni.

https://p.dw.com/p/1J76v
Großbritannien Schatzkanzler George Osborne Herbstansprache
George Osborne lokacin wani jawabi a gaban majalisar dokoki da ke birnin LondonHoto: picture-alliance/empics

Sakataren kudin Birtaniya George Osborne ya ce 'yan Birtaniya ka iya fuskantar karin kudaden haraji idan kasar ta kada kuri'ar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai EU. Ya ce matakin ficewar zai yi illa ga harkokin zuba jari da tattalin arziki da kuma zamatakewar iyali a kasar. A lokacin da yake magana a birnin London Sakatare Osborne ya ce dole ne a kara kudin haraji kuma gwamnati za ta rage yawan kudaden da take kashewa idan Birtaniyar ta fita daga Tarayyar Turai. Sakataren kudin ya ce dole kasar ta samar da wani kasafin kudi na gaggawa da zai tanadi tsuke bakin aljihu, matukar 'yan kasar suka kada kuri'ar amincewa da yin bankwana da kungiyar EU a kuri'ar raba gardama da za su kada a ranar 23 ga watan nan na Yuni. Binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar bayan nan ya nuna yawan masu goyon bayan a fita daga EU na karuwa.