1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May za ta kai ziyara Afirka

Yusuf Bala Nayaya
August 27, 2018

May za ta kasance firaministar Birtaniya ta farko da za ta sanya kafarta a Kenya tun bayan zamanin Margaret Thatcher da ta ziyarci kasar a 1988.

https://p.dw.com/p/33qTH
England Premierministerin Theresa May
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Dunham

Firaminista Theresa May ta Birtaniya za ta kai ziyarar kwanaki uku zuwa Afirka a wannan mako, ziyarar da ke zama ta farko tun bayan da ta hau mukaminta a 2016, wannan ziyara dai na da kudiri ne na inganta dangantakar Birtaniya da kasashen na Afirka idan ta kammala da ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai.

May za ta samu rakiya ta ministoci da wakilan 'yan kasuwa 29 daga masana'antu dabam-dabam, za su kuma ziyarci kasashen Afirka ta Kudu da Najeriya da Kenya kamar yadda ofishin firaministar da ke a titin Downing Street ya bayyana a wannan Litinin.

Za dai ta kasance firaministar Birtaniya ta farko da za ta sanya kafarta a Kenya tun bayan zamanin Margaret Thatcher da ta ziyarci kasar a 1988.