1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Italiya Silvio Berlusconi zai yi murabus a ranar talata

April 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0D

Makonni 3 bayan kaye da jam´iyar sa ta masu matsakaicin ra´ayin mazan jiya ta sha a zaben ´yan majalisar dokokin Italiya, FM Silvio Berlusconi ya ba da sanarwar yin murabus. Kamar yadda ofishin FM ya nunar, a ranar talata mai zuwa Berlusconi zai mikawa shugaban kasa Carlo Azeglio Ciampi takardunsa na yin murabus. A zabukan da aka gudanar a ranakun 9 da 10 na wannan wata na afrilu kawancen jam´iyar da ya ke wa jagora ta sha kaye a hannun jam´iyar masu matsakacin ra´ayin sauyi karkahin jagorancin shugaban ´yan adawa Romano Prodi. Yanzu haka sai an kammala zaben shugaban kasa sannan za´a fara shirye shiryen kafa sabuwar gwamnati karkashin Prodi, bayan da majalisar dokoki ta amince da zai fara shirin kafa sabuwar gwamnati. A ranar 18 ga watan mayu wa´adin mulkin shugaba Ciampi yake karewa.