1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Lesotho ya fasa komawa gida

September 2, 2014

Musayar wuta a tsakanin masu gaba da juna na kan gaba cikin dalilan da suka hana firaminista Thomas Thabane komawa gida a ranar Talatannan.

https://p.dw.com/p/1D5NT
Tom Thabane Premierminister von Lesotho
Hoto: picture-alliance/dpa

Firamnistan kasar Lesotho Thomas Thabane ya dage batun kowarsa gida a ranar Talatannan bayan gudun hijira na tsawon kwanaki uku a kasar Afirka ta Kudu, bayan masu shiga tsakani na yankin sun cimma matsayar mayar da shi kan mukamunsa, sakamakaon wani yunkurin kifar da gwamnati da sojoji suka yi.

Rashin komawar firaministan na zuwa ne adaidai lokacin da ake samun rahotannin musayar wuta a wasu sassan kasar.

Wani na kusa da mista Thabane ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa dalilai na tsaro su za su sanya a sami jinkiri na shirin komawar firaministan dan shekaru 75 zuwa wannan kasa ta shi da ke makwabtaka da Afrika ta kudu.

Da sanyin safiyar ranar Asabar Thabane ya tsere bayan sojoji sun mamaye shelkwatar hukumar 'yan sandan kasar. Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma da wakilan gwamnatocin yankin suka warware rikicin kasar ta Lesotho.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu