1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firayim ministan Kasar Mali ya kai ziyarar bazata a GAO

April 11, 2013

A karon farko tun bayan da dakarun Faransa suka kaddamar da kai hare hare a Arewacin Kasar Mali, Firaministan Kasar ya kai ziyara yankin.

https://p.dw.com/p/18EPs
Dakarun Kasar Mali dana Faransa na dakon Shugaban Kasar Faransa a yayin daya kai ziyara Kasar.Hoto: Reuters

Firaministan Kasar Mali Diango Cissoko ya kai wata ziyarar bazata zuwa Garin GAO dake Arewacin Kasar domin ganawa da Sojojin Kasar Faransa da kuma Na Afrika dake kokarin fatattakar masu kaifin kishin Addini da suka mamaye Arewacin Malin.

Wanna ziyara da Cissoko yakai Garin na GAO dai ita ce karon farko daya taba kaiwa a Yankin dake da tazarar kimanin Kilomita Dubu daya da Dari biyu da Bamako babban Birnin Kasar tun bayan da dakarun Kasar Faransa suka kaddamar da yaki a watan Janairun daya gabata domin dakile yunkurin da masu kaifin kishin Addini ke yi na shiga Bamakko.

A hannu guda kuma babbar Jam'iyyar Kasar Alliance for Democracy ta zabi Dramane Dembele daya daga cikin na hannun daman Gwamnatin rikon kwaryar Kasar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a karakashin Jam'iyyar.

Ba'a dai sanya takamaiman ranar da za'a gudanar da zaben ba, sai dai Gwamnatin rikon Kwaryar Kasar ta Mali karkashin Shugaba Diocounda Traore ta sanar da cewa za'a gudanar da zaben a watan Juli mai zuwa biyo bayan matsin lamba daga Kasashen Duniya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar.
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe.