1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fito na fito da Soji da 'yan Boko Haram

January 2, 2013

Rundunar tsaro ta hadin-gwiwa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Borno da ke arewacin Najeriya ta JTF ta ce ta kashe 'yan Boko Haram 13 a garin Maiduguri.

https://p.dw.com/p/17C8E
A picture taken on April 18, 2011 shows Nigerian police enforcing a curfew in the capital of Bauchi state, nothern Nigeria, after riots, run by muslim youth, broke out in Bauchi. Nigeria's Goodluck Jonathan has been declared winner of presidential elections in a landmark vote that exposed regional tensions and led to deadly rioting in the mainly Muslim north. Jonathan, the incumbent and first president from the southern oil-producing Niger Delta region, won 57 percent of the vote in Africa's most populous nation, easily beating his northern rival, ex-military ruler Muhammadu Buhari. AFP PHOTO / Tony KARUMBA (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP/Getty Images)
Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in BauchiHoto: Getty Images/AFP

Mai magana da yawun runduran ta JTF Laftanar Kanar Sagir Musa ya ce mutanensu sun yi ba takashi da 'yan bindigar ne a jiya Talata inda su ka samu nasarar karbe makamai daga hannu wasu daga cikinsu sai dai yayin arangamar, kakakin na JTF ya ce soja guda ya rasa ransa.

Laftanan Kanar Sagir Musa ya ce arangamar da su ka yi da 'yan Boko Haram din ta samo asali ne bayan da 'yan kungiyar su ka tada bam a wani shingen biciken ababan hawa na JTF inda soji su ka maida wuta.

Kawo wannan lokacin 'yan kungiyar ta Boko Haram ba su ce komai ba game da artanbun da sojin su ka ce sun yi da mutanen na su a jiya.

Rikici tsakanin 'yan kungiyar da jami'an tsaro a tarayyar ta Najeriya dai ta yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama musamman ma dai a arewacin kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman