1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fiye da mutane 3000 suka rasu a tekun Meditareniya a shekara ta 2014

December 24, 2014

Cikin sa'oi 24 da suka gabata an gano mutane 1,026 da ke son yin gudun hijira ta cikin tekun Meditareniya, inda mutane dubbai ke rasuwa a irin wannan kasada.

https://p.dw.com/p/1E9gP
Flüchtlinge in Lampedusa Italien Februar 2014
Hoto: picture-alliance/Ropi

Mahukuntan kasar Italiya sun bayyana samun mutane 1,026 a raye sannan guda biyar a mace a yayin wani sintirin aikin ceto da suka yi a tekun Meditareniya cikin sa'oi 24 da suka gabata.

A cewar mahukunta an shigar da gawar wani mai gudun hijirar zuwa jirgin Etna na sojan Italiya daga wani jirgin 'yan kasuwa, yayin da aka shigar da wasu matattun hudu a jirgin sintirin Orione na Cyprus.

Hukumar da ke lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a farkon wannan wata cewa kimanin masu neman tsallakawa Turai da ke ratsawa ta tekun na Meditareniya 3,419 sun halaka tun daga watan Janairu, abin da ya sanya wannan hanya ta zama mafi hadari wajen lakume rayukan mutanen.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo