1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin sake salon yakar ta'addanci a Sahel

Ramatu Garba Baba
December 4, 2019

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya mika goron gayyata ga shugabanin kasashen G5 Sahel da zummar sake zama don lalubo sabbin matakan yaki da ta'addanci da ya hana zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/3UEiZ
Gipfeltreffen in Bamako Mali
Hoto: Reuters/L. Gnago

Shugaba Macron ya ce yana son ya fahimci inda aka sa gaba da kuma irin tallafin da ya dace Faransa ta bayar a aikin da take na son ganin an kawo karshen aikin ta'addanci a yankin na Sahel. Faransa na fatan ganin nan bada jimawa ba, shugabanin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritaniya da kuma Nijar, sun fayyace wa duniya bukatunsu da irin shirin da suka yi da kuma taimakon da suke nema daga kasashen yamma.

Wannan dai na zuwa ne, kwanaki kalilan da gudanar da jana'izar sojojin Faransa goma sha uku da suka halaka a yayin da suke shawagi na sintirin tsaro a kasar Mali. Ya kasance rashi mafi girma da Faransan ta tafka tun bayan da ta tura sojojinta Mali a shekarar 2013 a yunkurin samar da zaman lafiya.