1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gabriel na son kasashen Larabawa su sasanta

July 3, 2017

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel yace batun tallafawa yan ta'adda da kudade shine ke tarnaki a rikicin Qatar da makwabtanta.

https://p.dw.com/p/2frK8
Saudi-Arabien Außenminister Sigmar Gabriel & Abdel bin Ahmed Al-Jubeir in Dschidda
Hoto: Getty Images/Photothek

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel yace za'a iya warware takaddamar da ke tsakanin kasar Qatar da makwabtanta na Larabawa ta hanyar cimma yarjejeniya a tsakanin kasashen yankin don dakatar da tallafawa yan ta'adda da kudade.

Gabriel wanda ya yi wannan bayanin a taron manema labarai tare da takwaransa na kasar Saudiyya Adel al-Jubeir a ziyarar da ya kai a yankin tekun fasha, yace baya tsammanin sauran kasashen Larabawa suna da wani shakku akan yancin Qatar na kasa mai cin gashin kanta.

A watan da ya gabata ne dai kasashe hudu da ke makwabtaka da Qatar ciki har da Saudiyya suka yanke huldar jakadanci dana kasuwanci da Qatar inda suke zarginta da tallafawa ayyukan ta'addanci zargin da Qatar din ta musanta.

Haka kuma sun bukaci Qatar din ta rufe gidan talabijin na Al Jazeera ta kuma kori sojojin Turkiyya daga cikin kasarta.

A halin da ake ciki Saudiyya ta baiwa Qatar karin wa'adin sa'oi 48 ta cimma sharuddan da aka gindaya mata idan ta na bukatar a sasanta.