1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Merkel da Issoufou kan matsalar bakin haure

Mahaman Kanta MAB
August 14, 2018

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou na ziyarar aiki a Berlin a ranar Laraba don ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da nufin duba hanyoyin magance fataucin bakin haure da ke bin Sahara don shiga nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/339bl
Der nigrische Präsident Issoufou in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa

Shekaru 55 da suka wuce ne magabatan Jamhuriyar Nijar da na Jamus suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hulda tsakaninsu. Kawo yanzu Nijar ta ci gajiya daga Jamus a fannoni dabam-daban ciki har da noma. Karancin abinci sakamakon rashin ingantar noman damuna da kasar ke fuskanta, ya sa sassa biyu bunkasa noman rani domin a samu yalwatar abinci a NIjar.

Sani Mahamadou Abdou Gao, jami'i a hukumar GIZ ta Jamus ya ce tun shekarun da suka gabata ne aka zabi jihohin Agadez ta Tahoua da Tillaberi a matsayin zakaran gwajin dafi na noman rani, kuma manoma 22 000 ne suka ci gajiya daga garuruwa 130.

Niger Agadez Bild 1 Konvoi mit Migranten verlässt Agadez
Matsalar bakin haure za ta mamaye tattaunawar Issoufou da MerkelHoto: DW/A. Kriesch/J.-P. Scholz

 A fannin yakar 'yan ta'adda karkashin rundunar G5 Sahel kuwa, gwamnatin Jamus ta taka rawar gani a Nijar wajen taimaka wa da dabaru da kayan aikin yakar masu tsananin kishin addini da ke kai hare-hare. Mohamed Bazoum, ministan da ke kula da harkokin cikin gida ya ce wannan ya ba su damar canza kamun ludayinsu a fannin yaki da fataucin miyagun kwayoyi da masu fasakworin mutane domin kai su Libiya da nufin shiga nahiyar Turai.

Wasu alkawaru da Jamus ta rattaba hannu a kansu da gwamnatin Nijar da suka hada da yaki da masu fataucin bakin haure da ke ratsa hamada zuwa Turai ba su shiga hannu ba tukuna.