1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Merkel da `yan adawan Rasha

January 17, 2006

A ziyarar da ta kai abirnin Moscow, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel ta yi shawarwari da shugabannin Rasha, sa'annan kuma ta gana da `yan adawan kasar, a wata liyafar da aka shirya mata a mazaunin jakadan Jamus a birnin na Moscow.

https://p.dw.com/p/Bu2M
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP

A ziyarar da ta kai a birnin Moscow dai, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, ba ta yi wata wata ba, wajen bayyana wa mai karbar bakwancinta, shugaba Vladimir Putin na Rasha, irin ra’ayinta dangane da batutuwan da suka shafi kare hakkin dan Adam. A tattaunawar da ta yi da shugaba Putin, ta takalo batun rikicin Checheniya da kuma arewacin yankin Caucasus gaba daya.

Bayan shawarwarin da ta yi da mahukuntan Rashan, shugaba Merkel ta kuma gana da wakilan kungiyoyi daban-daban na `yan adawa da kuma masu fafutukar kare hakkin dan Adam a kasar. Su dai `yan adawan sun yi kakkausar suka ga irin huldar da shugaba Putin ya kulla da tsohon shugaban Jamus Gerhard Schröder. Kamar dai yadda kakakin kungiyar, Ludmila Alexejwa, ya bayyanar:-

„Ba daidai ba ne, idan shugabannin muhimman kasashe biyu, masu dimbin yawan jama’a, suka mai da huldar da ke tsakanin kasashensu kamar wata alaka tasu ta bayan fage.“

Mafi yawan `yan adawan dai na ganin shugaba Putin da Gerhard Schröder, sun yi amfani da mukamansu ne wajen inganta huldodin abokantakar da ke tsakaninsu. Sukar dai dai na zuwa ne ga tsohon shugaban na Jamus, Schröder, wanda suka ce a duk ziyarce-ziyarcen da ya kai a birnin Moscow, bai taba cewa uffan game da halin da `yan adawan ke ciki ba. Vladimir Ryschkow, shugaban jam’iyyar adawa ta Repulican Party, cewa ya yi, game da bambancin da yake gani tsakanin tsohon shugaba Schröder da kuma shugaba mai ci yanzu Angela Merkel:-

„Ita dai shugaba Merkel ba irin wasannin motsa jikin nan a kan kankara suka fi damunta ba, ko kuma cin burodin da aka shafa wa kwan kifin nan da ake matukar sonsa a Rasha, wato Kaviar. Burinta ne ta ga an sami kyakyawar hulda tsakaninta da mahukuntan Rasha da kuma al’umman kasar ma gaba daya.“

Duk `yan adawan dai sun nuna gamsuwarsu da ganawar da suka yi da Angela Merkel, musamman ma dai ganin cewa, ta iya rashanci sosai, kuma sun yi tattaunawarsu ne cikin wannan harshen ba tare da wani tafinta ba. Hakan dai ya gamsad da su kwarai, inji Asenij Roginski, daya daga cikin shugabannin `yan adawan:-

„A nawa ganin dai, wannan matar, wato Merkel tana da kuzari kwarai da gaske. Ban sani ba dai ko za ta iya ci gaba da wannan kuzarin har karshen aikint. Rasha fa idan mutum ya saba da ita, da wuya kuma, ya taba mantawa da ita.“

To ko Merkel za ta iya jan jiki daga Rashan, a daura da yadda wanda ta gada, wato shugaba Schröder ya yi, ba za a iya sani ba tukuna a halin yanzu. Tabbas ne dai cewa, za ta sake saduwa da shugaba Putin a kalla sau uku a cikin wannan shekarar. Babu shakka, shugaban na Rasha, bayan ganawarsa da Merkel, ya fahinci cewa, ba wata sabuwar manufar siyasa Jamus za ta tinkare shi da ita ba, sai dai za a sami sauyi ne a salon tafiyad da wannan manufar.