1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Rikicin gwamnati da masarauta

Abdul-raheem Hassan
June 6, 2019

Gwamnan jihar Kano a Tarayyar Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa sarkin Kanon Muhammadu Sanusi na biyu wa'adin sa'o'i 24 ya ba da ba'asi akan zargin almubazzaranci da kudin masarauta.

https://p.dw.com/p/3Jzae
Nigeria - Emir von Kano - Muhammadu Sanusi II
Hoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Fadar masarautar Kanon dai ta tabbatar da karbar wasikar neman ba'asin da wa'adin ke kunshe a ciki, amma ta ce za ta nazarcin wasikar kafin daukar mataki na gaba. Sai dai masana shari'a kamar Barrister Audu Bulama Bukarti lauya mai zaman kansa, na cewa "Hukumar ba ta da hurumin binciken sarki, doka ta ce hukumar ta binciki ma'aikatan gwamnati ne kawai."

A gefe guda kuma gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da sarkin Maru Abubar Ibrahim mai daraja ta farko da hakimin Kanoma bisa zarginsu da alaka da 'yan bindigar da suka addabi jihar.