1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin duniya don tallafin Yemen

Abdourahamane Hassane
April 25, 2017

Da fara taron kasashen duniya a Geneva don samar da wata gidauniya domin taimaka wa al'ummar Yemen kungiyoyi agaji da ke aikin jinkai sun bayyana cewar al'ammura na iya kara rincabewa.

https://p.dw.com/p/2bttO
UN Geberkonferenz Jemen in Genf Guterres, Wallstrom und Burkhalter
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Flauraud

Akwai bukatar bayar da tallafin na gaggawa na kasa da kasa domin kawo karshen matsalar karancin abicin da ke haddasa tamowa ga yara kankana a kasar ta Yemen baki daya, da rashin magunguna a cikin asibitoci wanda yakin da ake yi ya janyo kamar yadda wakilan kungiyoyin agaji na Care International da ke a aiki a Yemen din suka bayana a farkon wannan mako a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus.

Kimanin mutane miliyan 17 'yan kasar ta Yemen ke bukatar agajin gaggawa, yayin da wasu miliyan bakwai ke fuskantar karancin abinci, sannan wasu kananan yaran na fama da tamowa akasari 'yan kasa da shekaru biyar, a cewar shugaban kungiyar ta CARE International Ralph Martens wanda ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da ya yi  ya ce  dole sai an kara samar da kudade domin kada al' amuran su lalace.

Jemen Leid der Kinder Flüchtlingslager bei Sanaa
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Ya ce Yemen na bukatar agaji kuma idan akwai lokacin da ya kamata a taimaka wa kasar shi ne yanzu domin ta na cikin matsanancin hali.

Majalisar Dinkin Duniya dai na bukatar kudade kusan biliyan biyu na Dalar Amirka  wanda zuwa yanzu aka samu sama da kashi goma na kudaden, kuma za a yi amfani da kudaden ne wajen sayan kayan abinci da ruwan sha, da samar da wuraren fakewa ga miliyoyin jama'ar da yakin ya rutsa da su wadanda ke bukatar agaji kusan kishi 60 cikin dari na yawa al'ummar kasar ta Yemen.

Unterernährung im Jemen
Hoto: imago/Xinhua

Wakilan na kungiyar Care International sun ce lamarin na yunwa wanda wasu kasashen irinsu Sudan ta kudu da Arewacin Najeriya da Somaliya da Yemen din na iya zama wani abu mafi daukar hankalin kungyoyin agaji na duniya a cikin  watanni na gaba masu zuwa.

Yakin da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen Houthi 'yan Shi'a da ke samun goyon bayan Iran da kuma gwamnatin 'yan Sunni mai samun goyo bayan Saudiyya tun a shekara ta 2015 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu goma kawo yanzu kamar yadda MDD ta bayyana, Sannan akwai dubbai da suka samu raunika.