1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin nuna adawa da tsadar rayuwa a Jordan

November 14, 2012

Bayan da jamiIan tsaro suka yi nasarar fasa taron nuna adawa da ƙarin farashin makami a Jordan ƙungiyoyin ƙwadago sun yi kira da a shiga yajin aikin gama gari.

https://p.dw.com/p/16jOR
Hoto: picture-alliance/dpa

Dubu dubatan 'yan ƙasar ta Jordan ne suka yi jerin gwano a kusan yawancin jihohin ƙasar a zanga zanga mafi girma dake nuna adawa da siyasar tattalin árziki da masarautar ƙasar ke bi. Masu zanga zangar sun yi ta rera waƙoƙi cewa "ba za mu sake biyan haraji jami'an gwamnati na rib da ciki kansa ba", a wani azanci da suke kan ƙara farashin makamashi da aka yi.

Zanga zangar da ta fara rikeɗewa zuwa neman sauyi, an kawo ƙarshenta ba tare da jikkata kowa ba, banda jami'an tsaro takwas da suka samu 'yan raunuka a yayin da suke fasa zaman dirshan ɗin da wasu masu fafutuka suka fara yi a dandalin Duwwar dake tsakiyar babban birnin ƙasar Amman.

Zargin jami'an gwamnati da cin dukiyar talakawa

'Yan kasa dai sun jima suna zargin jami'an gwamnati da yin sama da faɗi da asusun gwamnati, kamar yadda suke zargin masarautar kasar da kau da kai wajen hukunta shafaffu da mai daga manya jami'an gwamnati.

A ƙoƙarinta na musanta wannan zargi, gwamnatin ta yankewa tsohon ministan cikin gida ɗaurin shekaru shida bayan da aka same shi da laifin handame makudan kuɗin ma'aikatar tsaron kasar, lamarin da wasu 'yan adawa ke cewa, ɗaurin da aka yi wa tsohon ministan tsaron na ɗaukan fansa ne daga abokan hamayyarsa, ba shi da wata alaƙa da yaƙar cin hanci da rashawa a ƙasar.

Jordanien Demonstration
Hoto: Reuters

"Zamu shiga a cikin wata annoba makamanciyar igiyar ruwan Tsunami, muddin ba a janye wannan sabon farashin ba. Ba bu ta yadda talakawan dake rayuwar hannu baka hannu ƙwarya, za su gamsu da bayanan da mahukunta ke yi, na tsuke bakin aljihu da tsimin kuɗi, bayan ta bayyana a sarari ana ganin yadda jami'an gwamnati ke facaka da kuɗaɗen jama'a."

Boren yi wa masarautar Jordan tawaye

Firaministan ƙasar Abdallah Soor dai ya zargi ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi ta ƙasar da ingiza jama'a su yi wa masarautar ƙasar tawaye, don cimma manufofinsu na siyasa, batun da jami'an ƙungiyar suka musata.

Jordanien Demonstration
Hoto: Reuters

"Ina mamakin yadda mahukuntan da suka gaza wajen ragewa talakawansu kaifin talauci, bayansu suna ta fantamawa, za su yi zargin cewa zanga zangar da talakawa ke yi ta neman abarsu su rayu cikin mutunci, za a ce tana da wata alaƙa da siyasa."

Tuni dai ƙungiyar malaman ƙasar ta ce ta shiga yajin aikin sai baba ta gani, don nuna goyan bayanta ga masu zanga zangar.

Masharhanta dai na hasashen cewa, zai yi wuya, ƙasar ta Jordan ta iya ci gaba da yin amfani da tsohon farashi, sakamakon tasirin da rikicin Siriya ya yi wa tattalin arzikinta, amma duk a haka ana asa ran hukumar za ta sassauto ta rage farashin, don riga kafin rikiɗewar zanga zangar ta koma ta neman sauyin gwamnati.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal