1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gano 'yan gudun hijira a Najeriya

Uwais Abubakar IdrisSeptember 22, 2014

Kungiyar gangamin nan ta "Bring Back Our Girls" ta gano fiye da mutane 700 da suka tserewa rikicin Boko Haram daga yankin Gwoza na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/1DH9k
Nigeria Flüchtlinge in Maiduguri
Hoto: picture alliance/AP Photo

A kokarin da suke na jawo hankalin mahukuntan Najeriya kan halin da mutanen da suka rasa mauhallinsu dalilin rikicin Boko Haram ke ciki, kungiyar ta "Bring Back Our Girls" ta ce ta gano mutanen ne a kauyen Kubaru da ke Abuja, inda ta gudanar da wani tataki zuwa wannan kauye. Tattakin da kungiyar ta Bring Back Our Girls ta yi dai ya samu rakiyar wasu 'yan jaridu inda suka kai ga gano mutanen da ke rayuwa a yanayi na kunci da rashin muhalli bayan da suka baro gidajensu a yankin Gwoza da Konduga dake Jihar ta Borno.

Mutane na bayyana yadda suka tsira

Tserewa rikicin ya kasance abin farin ciki ga wadannan mutane duk kuwa da halin kuncin da suke ciki a yanzu. Pastor Usman David ya bayyana yadda ya samu tserewa zuwa kauyen na Bukuru a jihar Nasarawa.

Nigeria Protest Boko Haram Entführung
Kungiyar "Bring Back Our Girls" na gangami a AbujaHoto: picture-alliance/AP Photo

‘'Abinda ya faru shine lokacin da ‘yan Boko Haram suka shigo Kondiga sun fara da ofishin ‘yan sanda suka kona mana coci da motata sai na gudu zuwa garinmu sa'annan na gudu zuwa Shuwa daga can ne na zo nan. Akwai mutanenmu da yawa da suka mutu wasu kuma suna kan duste in sun sauko zasu fada hannun Boko Haram wasu suna mutuwa''.

Duk da cewa wadanan mutane suna rayuwa a yanayi da babu kyakkyawan muhalli ga rashin samun dauki daga gwamnatin amma ga daya daga cikin matan da ke tsugune tare da 'ya'yanta babu tunanen sake komawa inda ta fito domin yadda taga gawarwarki a yashe kere na ci kwari na ci mutane suna rubewa a wurin.

Nigeria Soldaten
Dakaraun Sojin NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo

Gwamnati bata san da zamansu ba

To ko gwamnatin Najeriya ta san da zaman wadannan mutane da har yanzu ba'a kai masu dauki ba? Hajiya Hadiza Sani ita ce kwamshiniya a hukumar kula da 'yan gudun hijira da mutanen da suka rasa muhallansu ta kuma ce...

‘'Bamu da masaniya da zamansu domin kuma ina jin har kungiyoyi masu zaman kansu basu san da zamansu ba, ai da wasu sun rubuto mana".

To sai dai ga Mallam Gambo Ungulu sarkin Kubaru ya ce tunda sojoji sun kai ga kamashi don ya baiwa mutanen mafaka yana ganin gwamnati ta san da zamansu. Kungiyar ta "Bring Back Our Girls" dai ta kaiwa mutanen kayan agaji tare da alkawarin bin matakan jawo hankalin hukuma domin a kai masu tallafi.