1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadi kan kara lalacewar siyasar Nijar

May 26, 2014

Rikicin siyasar Nijer da ya ki ci yaki cinyewa ya fara daukar wani sabon salo inda sannu a hankali yake rikida daga cacar baka zuwa na kan hare-hare.

https://p.dw.com/p/1C5wj
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Rikicin siyasar Nijer da ya ki ci yaki cinyewa ya fara daukar wani sabon salo inda sannu a hankali yake rikida daga cacar baka zuwa na kan hare-hare. A kan haka ne a jihar Tawa malaman addinai ke kira ga dukan bangarorin da su kai zuciya nesa tun lamarin bai yi kamari ba.

Gani ga wane dai ya isa wane jin tsoron Allah inji 'yan salon magana, domin kuwa akwai misalai da dama daga kasashen Afirka irinsu Kenya,Laberiya, Cote d'Ivoire da ma makwafciya Najeriya, inda rikice-rikicen siyasa suka yi sanadiyyar salwantar dubban rayukan jama'a. Wannan sabon yanayin na kai hare hare ga 'yan siyasa da ma cibiyoyin jam'iyunsu, wani bakon abu ne ga kasar ta Nijer shekaru kusan 23 da kasar ta rungumi tafarkin demokradiya . Kasancewarta a matsayain kasar da ake bayana mai yawan musulmai inda kusan kashi 99 daga cikin 100 musulmai ne ya sa a duk mlokacin da kasar ke nuna alamomin fitintunu,malaman addinai ke tsoma yayunsu ta hanyar jan hankali da nasihohi ga magabata tare da neman sauran jama'a dasu rakka kasar da addu'o'i inji Malam Moussa Souleiman.

Malaman addinan dai walau na Musulunci ne walau na Kirista, nada karfin fada a ji a jamhuriyar Nijer inda kundin tsarin milkin kasar ya baiwa kowane dan kasa damar shiga addininsa ba tare da tsongwama ba,wannan ne yasa Marus wani malamin addinin Kirista tofa albarkacin bakinsa.

Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Shugaban majalisar dokokin Nijar Hama Amadou(tsakiya)Hoto: DW/M. Kanta

Su ma dai magada al'adun gargajiya musamman matsafa, sun gargadi 'yan siyasar da su guji tsunduma kasar cikin halin ni 'yasu, kamar yadda matsafi Sha'aibu Dagarka ke cewa.

Tarihi dai ya nuna a duk lokacin da fadace-fadace ke barkewa, matasa ne a sahun gaba abunda yasa Adamou Hassan, wani jagoran kungiyar matasa ya kira matasan kasar da su nuna kin amincewarsu ga duk dan siyasar da zai amfani da su a matsayin 'yan bangar siyasa. Abun jira a gani dai shi ne yadda 'yan siyasan kasar zasu karbi kiraye kirayen domin dasa aya ga wannan guguwar dake zaman mace mai ciki ba a san abin da zata haifa ba.

Mawallafi: Yusufi Mamane
Edita: Umaru Aliyu