1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta halaka mutane fiye da 100 a Kwango

Usman Shehu Usman SB
September 28, 2018

A Najeriya 'yan bindiga dauke da makamai sun farma wani jirgin ruwan kasar Switzerland kana cutar Ebola ta halaka fiye da mutane 100 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/35epk
Straße von Malakka Frachtschiff
Hoto: Getty Images/A. Ross/Team Alvimedica/Volvo Ocean Race

Jaridar Jamus ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi kan matsalar fashi kan teku a Najeriya, inda jaridar ta ce a karshen makon da ya gabata 'yan bindiga dauke da makamai suka farma wani jirgin ruwan kasar Switzerland wanda ya taso daga birnin Lagos zuwa Fatakwal (Port-Harcourt). Jaridar ta ce 'yan fashin da suka dira kan jirgin nan take suka yanke wayoyin sadarwa, kana suka tsare daukacin ma'aikatan jirgin 19.  jirigin mai suna Glarus an kera shi ne a shekara ta 2001, don haka yana daga cikin manyan jiragen dakon kaya na zamani da ake ji da su, inda yake iya dokon kaya sama da ton 46,500.

Niger - Hirseballen im Dorf Tapkin Marke
Hoto: picture-alliance/ZB

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung ta yi sharhi ne kan Jamhuriyar Nijar. Jaridar ta ce Tony Rinaudo  dan kasar Ostiraliya ya samu kyautar kwatankwacin ta Nobel bisa tallafi ga harkar noma a Jihar Maradi. Tony Rinaudo ya zabi kauyen Dan Indo, kauyen da ya yi fama da matsalar fari abin da ya haddasa yunwa yankin sakamakon rashin samun kayan gonaki. Amma yanzu bisa tallafin wannan dan kasar Ostiraliya ya sa 'yan kauyen sun manta da batun matsalar gona duk da cewa ba a samun ruwan samam mai yawa. A cewar Sule Lebo wani mazaunin kauyen na Dan Indo, a baya tsakanin garinsu da titin da ke ake bi wanda ke da kilo mita biyu babu abin da ake gani illa yashin hamada, amma yanzu bisa tallafin Tony Rinaudo  ba abin da ake gani sai bishiyoyi, kuma dalilin hakan yakin baki daya kasance mai cike da inuwa duk da zafin da ake tabkawa. Dan shekaru 61 Tony Rinaudo bisa wadannan ayyukan da ya yi ya saka kungiyoyin kasa da kasa suka shada da kokarinsa abin da ya sa aka ba shi kyautar kwatankwacin ta Nobel.

Kongo Ebola
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo

Sai jaridar die Tageszeitung, inda ta yi sharhi kan bala'in da yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke fuskanta. Jaridar ta ce tarin mutattu da kuma jini da ke kwarara su ne hotunan da ake gani suna fitowa daga yankin gabashin Kwango, sakamakon fadace--fadace tsakanin 'yan bindiga, to sai dai yanzu an samu mace-mace a garin Beni da ke jihar Arewacin Kivu sakamakon annobar cutar Ebola. Jaridar ta ce bisa alkaluman da ma'aikatar lafiya ta kasar Kwango ta fitar, a birnin Beni da kewaye sama da mutane 151 suka kuma da cutar Ebola daga ciki sama da 100 tuni suka mutu sakamakon cutar ta Ebola. Sai dai babbar matsalar ita ce, likitoci da sauran ma'aikatan agajin gaggawa na fuskantar matsalar isa yankin sakamakon farmakin 'yan bindiga.

Wartende Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/C. Stache

A sharhinta jaridar Neues Deutschland ta duba matsalar da 'yan gudun hijra na kasar Iritiriya ke fuskanta, duk da cewa sun samu ficewa daga kasar har suka isa kasashe irin Jamus. Jaridar ta ce sun yi hijira bisa ukubar da gwamnatin kama karya ke gallaza musu, amma kuma a bisa tilas suke agaza wa wannan gwamnati. Misali akwai tsarin da kasar Jamus ta fitar na tallafa wa 'yan gudun hijira da ake son mayarwa kasashensu, to amma dole sai kowa ya gabatar da shaidar cewa shi dan wannan kasar ne, don haka ga 'yan kasar Iritiriya da ke son neman takardun tafiya a ofishin jakadancinsu dole sai sun biya wani haraji da gwamnatin kama karya a Asmara ta azawa duk dan kasar da ke zama a ketare.