1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garumbawul ga shugabannin sojojin Sudan

February 27, 2018

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya yi garumbawul ga shugabannin sojoji da sauran hukumomin tsaro na kasar.

https://p.dw.com/p/2tQTt
Sudan Omar Hassan Ahmad al-Bashir
Hoto: picture-alliance/AA/E. Hamid

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya fatattaki babban habsan sojojin kasar Lantanar Janar Emadeddin Adawi daga bakin aiki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito. Sannan an bayyana sunan Laftanar Janar  Kamal Abdul Maaruf a matsayin sabon babban habsa na sojojin kasar.

Kana Shugaba Hassan al-Bashir ya ya yi sauye-sauyen shugabannin sauran hukumomi na tsaron kasar ta Sudan da suka hada da hukumar leken asiri.