1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar cin kofin kwallon Tennis a Madrid

May 17, 2017

Rafael Nadal dan kasar Spain ya lashe kofin bayan da ya doke Dominic Thiem dan kasar Ostriya.

https://p.dw.com/p/2d6gN
Tennis - Barcelona Open Final Rafael Nadal
Hoto: Reuters/A. Gea

A fagen gasar kwallon Tennis ta Master 1000 ta birnin Madrid, Rafael Nadal dan kasar ta Spain ya lashe kofin bayan da ya doke Dominic Thiem dan kasar Ostriya da ci (7-6, 9-7, 6-4) . Wannan nasara ta bai wa Rafael Nadal damar komowa a matsayin na hudu a kakar wasannin Tennis ta bana inda Andy Muray na Birtaniya ke sahun gaba a yayin da Novac Djokovic dan kasar Sabiya ke a matsayin na biyu.

A bangaren mata kuwa Simona Halep 'yar kasar Rumaniya ce ta lashe gasar ta birnin Madrid  bayan da ta doke Kristina Mladenovic 'yar kasar faransa a karawar karshe. A yanzu Angelika Kerber 'yar kasar Jamus ke kan tebirin gasar kwallonTennis ta bana a yayin da Serena williams da ke rike da kambun ta koma a matsayin ta biyu.