1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar kwallon kafa na duniya

June 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buuo

A yau ne zaá buɗe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya a birnin Munch dake nan Jamus. Shugaban ƙasar Jamus Horst Kohler zai fara doka kwallo domin buɗe gasar bayan kasaitaccen bikin kaddamar da wasannin. A wasan da zaá buga na farko a yau Zaá kara ne tsakanin Jamus da Costa Rica a birnin Munich. Sai dai kuma ƙungiyar kwallon ƙafar ta Jamus zata buga wasan ne ba tare da Kaftin ta Michael Ballack ba saboda bai gama warkewa daga raunin da ya ji a gwiwar sa ba. A cewar mai koyar da wasa na ƙungiyar ta Jamus, Juergen Klinsman, rashin kaftin din, babban koma baya ne ga ƙungiyar kwallon kafar ta Jamus wadda ke fatan samun nasarar cinye kofin na duniya. A yau ɗin dai kuma, zaá kara tsakanin ƙasar Poland da Ecuador a filin wasa na Gelsenkirchen. Yan kallo miliyan uku ne tare da baƙi miliyan ɗaya daga ƙasashen ƙetare ake sa ran za su kalli gasar wasannin wanda zaá shafe tsawon wata guda ana gudanarwa. ƙungiyoyi 32 ne zasu kara a gasar wasannin a filayen ƙwallon ƙafa guda goma sha biyu a nan tarayyar Jamus. Zaá buga gasar ƙarshe a birnin Berlin a ranar 9 ga watan Yuli.