1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

gazawar mahukuntan Amurka

September 2, 2005

Mahukuntan Amurka sun nuna gazawa wajen kai taimako ga mutanen da mahaukaciyar guguwar nan ta "Katrina" ta rutsa dasu

https://p.dw.com/p/BvZx
Tagayyararru daga guguwar katrina
Tagayyararru daga guguwar katrinaHoto: AP

Mahaukaciyar guguwar ta Katrina ta haddasa mummunar barna fiye da yadda ake zato. Ire-iren wadannan bala’o’i daga Indallahi kann jefa dan-Adam cikin hali na kaka-nika-yi da rashin sanin tabbas a game da makomarsu, kamar dai tsautsayin nan na tsunami a yankin kudu-maso-gabacin Asiya. To sai dai ita wannan guguwar ta banbanta da wadda aka fuskanta a Indonesiya da Sri Lanka, saboda ta shafi wata kasa ce da tafi kowace ci gaban masana’antu a duniya, wadda ke da nagartattun hanyoyin sadarwa da wadatar arziki da kuma fice wajen tinkarar ire-iren wannan mahaukaciyar guguwa. A saboda haka ya zama abin mamaki ganin cewar kwanaki hudu bayan afkuwar wannan tsautsayi har yau ana ci gaba da fama fa yamutsi da rashin sanin tabbas a yankunan da bala’in ya rutsa dasu. Wani abin lura a nan shi ne dubban ‚yan sa kai da kwararrun ma’aikatan taimako suna bakin kokarinsu wajen ceton jama’a ba dare-ba-rana duk da mawuyacin halin da ake ciki, inda ruwa yayi awon gaba da gadoji da tituna a yankin da bala’in ya rutsa da shi a fadin murabba’in kilomita dubu 140 tare da bannatar da dukkan hanyoyin sadarwa a yankin. Amma duk da haka wajibi ne a saka ayar tambaya a game da dalilin da ya sanya gwamnatin shugaba Bush tayi wa lamarin rikon sakainar kashi har sai da al’amura suka nemi zama gagara-badau kafin ta mayar da martani wajen taimaka wa mutanen da tsautsayin guguwar ya rutsa dasu. Wai shin me sojojin Amurka suke yi ne a sa’o’in farko da suka biyo-bayan bala’in, lokacin da ake bukatar taimako daga garesu domin ceto mutanen da ke kaka-nika-yi da ruwan da ya mamaye gidajensu ko kuma toshe madatsan ruwan New Orleans? Ita kanta ta’asar ‚yan kwasar ganima da ta biyo baya, inda akan idanun jami’an tsaron Amurka suke wawason dukiyar mutane, da tun da farkon fari ya kamata a karya alkadarinsu. Abin kunya ma shi ne ganin yadda Amurka ke nuna karfin hatsi a kasashe na ketare, amma a cikin gida jami’an tsaronta suka ba da kai bori ya hau ga ‚yan ta-kife dake wawason ganima, kana a daya hannun kuma suka gaza wajen kwashe mutanen da bala’in ya rutsa dasu domin kai su tudun na tsira. Dubban mutane suka tagayyara a yankin Superdome na New Orleans tsawon kwanaki da dama suna fama da zafin rana mai tsanani da rashin ruwan sha mai tsafta. Birane da dama suka bayyana shirinsu na karbar ‚yan gudun hijira, amma mahukuntan Amurka sun gaza kwashe su zuwa wadannan yankuna. Wannan kadan ne daga gazawa da rashin tabuka kome na hukumar ceton rayuka ta kasar Amurka. Amma duk da haka wannan bala’in ya isa zama gargadi ga shugaba George W. bush, wanda ke fatali da dukkan manufofi na kare kewayen dan-Adam.