1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Harkokin noma ta kafofin sadarwar zamani

Maxwell Suuk/ ARHJune 22, 2016

Tsarin na nadar bayanan manoma a wayar salula don rage almundahanan kayayyakin inganta noman da saukaka ayyukan malaman gona.

https://p.dw.com/p/1JBO0
São Tomé Fair Trade Kakao
Hoto: DW/Ramusel Graça

A bara ne dai ma'akatar gona da abinci ta kasar Ghana ta bllo da sabon tsarin samar da bayanai a kan harkokin noma da ake kira E-Agriculture. Wannan tsarin na samar da sabbin dabarun noma da muhimman bayanai ta wayar salula ba tare da biyan ko sisi ba. Abukari Fuseini na cikin manoma miliyan uku da ke cin gajiyar tsarin na E-Agriculture a yanzu haka.

Ya ce: "Kawo yanzu dai kwalliya na biyan kudin sabulu, ganin yadda sabon tsarin na E-Agricultre ke bamu damar sanin sabbin dabarun noma. Ko da ka samu matsala a cikin gonarka, kana da damar kiransu kai tsaye kuma ka samu mafita nan take."

Shi ma dai wannan manomi Ibrahim Mahama ya yaba da sabon salon ganin yadda a baya harkokin noman ke basu wahala.

Ya ce:"In da ba don zuwan wannan sabon tsarin samar da bayanai na zamani ba, da za mu cigaba da dandana kudarmu kamar a baya, na rashin sanin hakikanin abin da ya da ce, to amma yanzu muna cikin manoman da ke farin ciki."

Ghana Gender Gewalt Majeed Zakaria will sich scheiden lassen, wenn seine Frau ihn wegen sexueller Gewalt anzeigt
Majeed Zakaria manomi a arewacin GhanaHoto: DW/M.Suuk

Gwamnatin kasar Ghana dai ta kirkiro da tsarin na E-Agriculture ne da nufin kau da matsalolin sace-sace da tsadar jigilar amfanin gona da manoman kasar ke fuskanta.

Kwalliya ta fara mayar da kudin sabulu

Baba Musah shi ne babban jami'in da ke kula da tsarin a shiyyar arewacin Ghana.

Ya ce: "A wannan nau'in mukan shigar da bayanan manoman a na'ura, sannan mu basu lambobin shaida da za su tura wa dillalai don samun taki cikin sauki. Ba kamar yadda muke shan wahala a baya da tsarin amfani da takardu ba."

Babban kalubale da sabon tsarin samar da bayanai ga manoman ta kafar sadarwar zamani shi ne sanin yadda za a yi amfani da tsarin ta wayar salula domin kimanin kashi 80 cikin 100 na manoman kasar ba su iya karatu ko rubutu ba. To amma tsarin ya tanadi dukkanin bayanai cikin harsuna dabam-dabam.

Gwamnatin Ghana dai ta yi yakinin tsarin na E-Agriculture ya habaka dangantaka tsakanin malaman gona da manoma, inda burin ma'aikatar noma da abinci ta kasar shi ne fadada tsarin ga sauran manoman karkara don inganta harkar noma da bunkasa samar da abinci a kasar.