Mutane 28 na samun jinya a asibiti
March 22, 2019Talla
Kwamandan rundunar 'yan sanda Joseph Antwi Gyawu ya shaidar da cewar, motocin biyu kirar Bus dauke da mutane 50 kowanne sun yi karo da juna, in da nan take daya ya kama da wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 60.
Jami'an agajin gaggawa dai sun kasance a wurin da hatsarin ya auku tare da masu kashe gobara domin bada dauki.
Kwame Arhin da ke zama likita a asibitin gwamnati na garin Kintampo, ya bayyana cewar akwai wasu mutane 28 da suka jikkata, bakwai daga cikinsu na cikin mawuyancin hali na jinya.