1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Rikicin kasuwancin baki da 'yan gari

Inshola Yussif Abdul Ganiyu YB
August 7, 2018

'Yan asalin Najeriya mafi akasari al'ummar Igbo sun koka da yadda ake rufe masu shagunan da ma manyan shugunan ajiyarsu ta karfi wani lokaci ma har da duka.

https://p.dw.com/p/32kJ0
Handwerker in Suame (Bildergalerie)
Hoto: DW/Y. Yeebo

Rikici ya barke tsakanin 'yan kasuwa na cikin gida a Ghana da 'yan kasuwa 'yan asalin Najeriya da ke kasuwanci a babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Suame a birnin Kumasi a jihar Ashanti, inda suke zargin 'yan asalin Najeriya da yin kasuwancin da ya saba wa ka'ida. 'Yan asalin kasar ta Ghana dai sun tilasta wa 'yan Najeriyar rufe shagunansu saboda a cewarsu ya kamata idan za su bude manyan shagunan ajiyar kayayyaki kamar na bangarorin kayan gyaran mota ya kamata a ce sun dauki ma'aikata 'yan asalin Ghana kamar ashirin amma basa yin hakan.

Handwerker in Suame (Bildergalerie)
Tsofaffin kayan mota su ke zama a gaba a wannan kasuwa ta SuameHoto: DW/Y. Yeebo

'Yan asalin kasar ta Ghana dai da suma ke siyar da kayayyakin gyaran motar wadanda al'ummar Igbo daga Najeriya ke masu aiki suma shagunansu ba su tsira ba domin ana rufewa, har sai gwamnati ta shiga tsakani don acewar 'yan kasuwar ta Ghana sun dade suna korafi kan batun amma gwamnati ba ta dauki wani mataki ba.

A nasu bangaren masu siyar da kayyakin 'yan asalin Najeriya mafi akasari al'ummar Igbo sun koka da yadda ake rufe masu shagunan da ma manyan shugunan ajiyarsu ta karfi wani lokaci ma har da duka idan mutum ya yi taurin kai.