1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta samu nasara akan Amirka

June 27, 2010

Ghana ta ganawa Amirka ƙwallaye biyu a raga ita kuma Amirka ta saka ƙwallo ɗaya a raga

https://p.dw.com/p/O4Fe
'yan wasan ƙwallon ƙafan GhanaHoto: dpa

Ƙasar Ghana ta nunawa ƙasar Amirka cewar ba wai kawai a tsarin demokiraɗiyya ne tayi fice ba harma da ƙwallon ƙafa. A jiya ta samu nasara akan ƙasar Amirka a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ke gudana a afirka ta kudu.

A wasan da ta buga jiya da Amirkan, Ghana ta ganawa Amirka ƙwallaye biyu a raga bayan da aka shafe mintuna 90 na wasa ana ɗaya da ɗaya. Bayan ƙarin wa'adin wasa da mintuna uku ne Ghana ta saka ƙwalo ta biyu daya bata nasarar wucewa zagaye na gaba ko kwata Final.

Wannan nasara data samu akan ƙasar Amirka yasa Ghana ta kasance ƙasa ta uku a nahiyar afirka data samu sukunin wucewa zagayen kwata final a tarihin gasar cin kofin duniya. Sauran ƙasashen afirka da suka taka irin wannan rawa sun haɗa da kamaru da kuma Senegal.

Yanzu Ghana zata haɗu da Uruguay wanda itama ta samu nasara akan Koriya ta Kudu da ci 2 da 1. A yau ne kuma ƙasashen Jamus da Ingila zasu fafa ta aci gaba da gasar cin kofin na duniya.

Tuni dai shugaban Amirka Barack Obama wanda ya kalli wasan a wajen taron ƙungiyar G20 da G8 a birnin Kanada ya aike da saƙon fatan alheri a shugaba Attah Mills na Ghana.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Madobi