1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka na neman samun tallafin kuɗaɗe daga Turai

Abdourahamane HassaneMarch 9, 2015

Ministocin kuɗi na ƙasashen Ƙumgiyar EU na tattauna shirin sauye-sauye na tattalin arziki da Girka ta gabatar musu gabanin samun tallafin kuɗaɗe biliyan bakwai.

https://p.dw.com/p/1Engm
Griechenland Yanis Varoufakis
Ministan kuɗi na Girka Yanis VaroufakisHoto: Reuters/E. Vidal

Ministocin na kuɗi na Eurogroupe na yin taro a birnin Brussels na Beljium domin tattauna batun sauye-sauyen na tattalin arziki da Girka ta yi alƙawarin yi gabanin samu kuɗaɗen tallafin domin kaucewa ƙasar ga faɗawa cikin wata matsalar kuɗi da ka iya janyowa ƙasar wani babban koma baya a kan sha'anin tatalin arziki.

Tsarin sauye-sauye na tattalin arziki da Girka ta gabatar ga taron

Wakilai na gwamnatin ta Girka sun gabatar ga taron ministocin tsarin da suka yi na yin sauye-sauyen na tattalin arzikin ƙasar.Ɗaya daga cikin sharuɗa mafi girma wanda yakamata gwamnati ta Girka ta cika gabanin samun kuɗaɗen da take buƙata aƙalla biliyan bakwai a cikin watan Afrilun da ke tafe idan har an daidaita. Tun can da farko dai gwamnatin Girka ta aike da jerin sauye-sauyen na tattalin arziki ga shugaban tawagar ta Eurogroupe Jeroen Dijsselbloem. Daga cikin abin da gwamnatin ta Girka ta tanada har da da shirin sayar da hannayen jari na kamfanoni malakar gwamnatin.

EU Jeroen Dijsselbloem Eurogruppenchef
Tawagar Eurogroupe tare da jagoranta Jeroen DijsselbloemHoto: AFP/Getty Images/J. Thys

Kuma waɗannan sauye-sauyen su ne wakilan banki Turai da na hukumar tsara kuɗaɗe ta duniya IMF za su duba su tattauna su ga abin da yakamata.Steffen Kampeter shi ne babban sakataran ƙasa na Jamus a ofishin ministan kuɗi.

''Wannan batu na ɗaya daga cikin batutuwan masu mahimmanci da ɓangarorin biyu za su yi ƙoƙarin samun fahimtar juna tare da bayyana ƙarara abin da shirin ya ƙunsa a tattaunawar.''

Girka na iya faɗawa cikin wani hali na rashin tabbas idan ba a daidaita ba

Ba shakka idan har ministocin kuɗin ba su gamsu ba da tsarin da Girka ta gabatar musu to kam tabbas Girkan za ta iya samun matsala kamar yadda ministan kuɗi na ƙasar ta Girka Yanis Varoufakis ya bayyana a ƙarshen makon jiya. Girka tana fama da basussuka da suka yi mata katutu waɗanda wa'adin biyansu ke kawo ƙarshe a ƙarshen wannan wata na Maris wanda aka ƙiesta yawansu cewar zai iya kai biliyan shidda na Euro. Simone Maria Peter shugabar jam'iyyar masu fafutukar kare muhali ta Jamus ta ce akwai abin da su suke da ra'ayi a kansa a kan batun na Girka.

Außerordentliches Treffen der Eurogruppen Finanzminister Eurogruppen Christine Lagarde
Taron ministocin kuɗi na Turai a gaba shugabar asusun IMF Christine LagardeHoto: picture-alliance/dpa/O.Hoslet

'' Shirin tsuke bakin aljihu wanda muka daɗe muna yin Allah wadai da shi ba ya gyara lamarin basusuka da ake bin ƙasa sai ma ƙarawa. Za a samu rashin aikin yi, na jama'a abubuwa za su daɗa yin tsanani maimakon a sararra.''

A wani bincike na hasashen ra'ayoyin jama'a da aka bayyana ya nuna cewar yawancin al'ummar Girka na buƙatar ganin gwamnatin Alexis Tsipras ta cimma yarjejeniya da Eurogroupe domin kaucewa ƙasar ta Girka ficewa daga cikin rukunin ƙasashen da ke yin amfani da kuɗin Euro.