1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damagaram ta samu tallafi daga GIZ

August 24, 2021

Hukumar Raya Kasashe ta Jamus wato GIZ, ta bayar da makudan kudi domin gyaran kayan tarihi a masarautar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3zQKn
Palast des Emirs von Damagaram in Zinder, Niger
GIZ za ta taimaka wajen yin gyara a masarautar Damagaram da ke Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Kayan tarihin na masarautar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar din da za a gyar dai, sun hadar da   Kasuwar Baya da Rijiyar Cimma da gidan kaso na gargajiya da ake kira da Gidan Tururuwa da Kofar Garu da dakunan matan sarki da kuma gidan Jamusawa tun na lokacin Heinrich Barth. Yayin ziyarar da ya kai a lungu da sako na masarautar Dakta Andreas König shi ne wakilin hukumar ta GIZ a Jamhuriyar ta Nijar, ya gudanar da ziyara don taya al'ummar yankin murnar farfado da kayan tarifin Daular da hakan ke kara dankon zumunta tsakanin masarautar da kuma kasar Jamus. Binciken kayan tarihin na Afirka dai na zaman abu mai matukar muhimmi ga Turawan mulkin mallaka, a cewar mai alfarma Sultan na Damagaram Alhaji Abubakar Sanda. A cewar  Madame Umaru Fatima Ali Hamidu jagorar shirin na GIZ a Damagaram, miliyan 29 ne na kudin sefa suka saka kuma matasa 10 da suka bai wa horo a fanin gine-gine ne ke aikin da aka dibarwa wa'adin kwanaki 90.