1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta hallaka mutane 14 a cibiyar nakasassun Jamus

November 26, 2012

Wata gobara da ta tashi ta hallaka mutane 14 tare da jikata wasu bakwai, a wata cibiyar aiyukan nakasassu ta Jamus.

https://p.dw.com/p/16qDo
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata gobara da ta tashi a wannan Litinin, ta hallaka mutane 14 tare da jikata wasu bakwai, a wata cibiyar aiyukan nakasassu da ke kusa da birnin Freiburg na nan kasar Jamus.

'yan kwan-kwana da ma'aikatan agaji sun ruga domin kai dauki, kuma sun samu nasarar ceto mutane masu yawa cikin ginin da wutar ta tashi. Wannan cibiyar da nakassaun ke gudanar da sana'o'i ta na da nisan kilo mita 40 gabashin birnin Freisburg kudu maso yammacin kasar. Akwai kimanin nakasassu 120 da ke gudanar da aiki cikin cibiyar.

Tuni karamin ministan cikin gina na Jihar Baden-Wuerttemberg Reinhold Gall ya nufi wajen da lamarin ya wakana.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi