1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudunmawar Jamus a Afirka ta Tsakiya

April 11, 2014

Gwamnatin Jamus ta amince da tura dakarunta zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin yin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, daidai lokacin da wutar rikici ta kabilanci da addini ke ci gaba da ruruwa.

https://p.dw.com/p/1BgdV
MedEvac Lazarettflugzeug der Bundesluftwaffe
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan mataki da mahukuntan na Jamus suka dauka dai ya biyo ya zo ne daidai lokacin da ake kiraye-kiraye na daukar kwararan matakai domin kawo karshen zub da jinin da ake a kasar. Na baya-bayan nan dai shi ne wanda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-Moon ya yi Lahadin da ta gabata lokacin da ya kai wata ziyara Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya inda ya ce duniya na dab da yin kuskure in ba tai abin da ya dace ba kan wannan rikici.

Gwamantin ta Jamus dai za ta aike ne da sojinta tamanin domin dafawa kimanin sojin EU 800 zuwa dubu 1000 da za su yi aiki a kasar musamman ma dai a Bangui da kuma filin jirgin saman kasar wanda wani bangare daga cikinsa yanzu haka ke zaman sansani na 'yan gudun hijira wanda galinsu musulmi ne.

Tallafi na jigilar marasa lafiya don yi musu magani

Zentralafrika Bangui Flüchtlinge 30.01.2014
'Yan gudun hijira a BanguiHoto: Reuters

Dakarun na Jamus dai za su gudanar da aiyyuka ne wanda ba su danganci fita filin daga ba kamar yadda Yvonne van Diepen, kwararriya kan kimiyyar siyasa a cibiyar harkokin waje ta nan tarayyar Jamus ta shaida, inda ta kara da cewar ''sojin Jamus za ta fi maida hankali ne kan abubuwan da suka danganci tallafi na zirga-zirgar jirage.''

Baya ga wannan agaji da Yvonne ta ce dakarun na Jamus za su bada, a hannu guda sojin za kuma su tallafawa takwarorinsu da suka samu raunuka don kaisu wajen da za a yi musu magani. Kazalika wasu sojin na Jamus za su kasance a cibiyar dakarun da za su yi aiki a Bangui din wadda za ta kasance a birnin Larissa na kasar Girka da kuma birnin Bangui.

Suka kan rawar da sojin Jamus za su taka a Bangui

Matsayi da gwamantin Jamus ta dauka na nesanta sojinta daga shiga fagen daga ya fara janyo suka daga ciki da wajen kasar, inda da dama ke cewar matsayin na mahukuntan Jamus zai kasance wani abun rashin jin dadi ga kasashen na Turai da za su yi karo-karon sojinsu da za su yi aikin na wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Entwicklungsminister Gerd Müller Bangui Zentralafrika
Gerd Müller a BanguiHoto: picture-alliance/dpa

Harald Kujat tsohon shugaban rundunar sojin Jamus na daga cikin 'yan kasar da ke ganin rashin dacewar shigar sojinsu a dama da su a fagen fama.

Ya ce ''idan mutun zai shiga a dama da shi a abu to ya kyautu a dama da shi a aiyyukan da ke da wuya. Takwarorinmu na Turai ba za su ji dadi a ce sojin mu za su takaita ne kawai ga kai wanda suka jikkata asibiti ba. Ya kamata a ce sojin Jamus sun shiga an fafata da su. Nesanta su da fagen daga abu ne da ba za a amince da shi ba.''

Shi ma dai guda daga cikin 'yan majalisar kungiyar tarayyar Turai ta EU Michael Gahler cewa yai ya kyautu Jamus ta taka bude hannunta wajen tallafawa dakarun na EU domin yanzu haka irin tallafin da ta bada ya kasa, sai dai gwamnatin ta Jamus na da'awar ta na bakin kokarinta, hasalima ta yi alkawarin bada tallafin euro miliyan 8 da rabi a matsayin agaji da kuma karin euro miliyan 1 da rabi don tallafawa wanda rikicin Bangui din ya daidaita.

Yanzu haka da al'ummar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da ma dai kasashen duniya na zuba idanu wajen ganin kamun ludayin rundunar ta EU wadda ta kunshi sojin Jamus da ma irin taimakon da za su bada wajen maido zaman lafiya a kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu