1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurbatacciyar allura ta hallaka yara a Juba

Yusuf Bala Nayaya
June 3, 2017

Yara goma sha biyar ne suka hallaka a Sudan ta Kudu sakamakon yi musu allurar kyanda wacce ta riga ta gurbata biyo bayan rashin ajiye ta cikin firji da ma amfani da sirinji guda wajan cakuda allurar.

https://p.dw.com/p/2e4ks
Südsudan Medienreise Aktion Deutschland hilft
Hoto: Aktion Deutschland Hilft/Max Kupfer

Baya ga tabargazar da aka tabka wajen cakuda allurar akwai kuma wasu yara biyu tsakanin shekaru 12 zuwa 13 da aka samu cikin jami'ai masu allurar a cewar Riek Gai Kok da ke zama ministan lafiya a kasar ta Sudan ta Kudu.

A cewar Kok sakamakon bincike da suka gudanar ya gano jami'an da rashin bin ka'idoji na amfani da allurar rigakafin na kyanda a tsawon kwanaki hudu da aka yi ana wannan aiki da aka yi wa kimanin yara 300 allurar a jihar Kapoeta da ke yankin kudu maso gabashi na kasar.

Kaddamar da kamfen din dai na yaki da cutar kyanda a Sudan ta Kudu na zuwa ne bayan da aka samu yara 70 sun hallaka a kasar sakamakon barkewar cutar ta kyanda a wannan kasa da ke a yanayin yaki sama da shekaru uku.