1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurfanar shugaban Kenya gaban kotun ICC

Salissou BoukariOctober 7, 2014

A Larabar nan ce (08.10.2014) shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai gurfana gaban kotun hukunta laifukan yaki da ke birnin Hague na kasar Holland.

https://p.dw.com/p/1DRcG
AU-Gipfel in Addis Abeba, Äthiopien, 31.01.2014 Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters

Gurfanar da Shugaba Kenyatta zai yi dai ta biyo bayan kai kararsa da aka yi dangane da tarzomar da ta wakana bayan zabukan da aka yi a Kenya din a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2008. An dai danganta wannan rikici da ya jawo rasuwar mutane da dama da shugaban na Kenya ko da dai ya musanta wannan zargi.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaba mai ci ya amince zai gurfana a gabanta. A bara ma dai kotun ta saurari Mr. Kenyatta ko da dai a wancan karon ya gurfana ne a matsayinsa na shugaban kasa sai dai yanzu zai gurfana a matsayinsa na Uhuru Kenyatta.

Fatou Bensouda
Fatou Bensouda - Babbar mai gabatar da kara a kotun ICCHoto: Reuters

Masu rajin kare hakkin Bil-Adama sun jinjinawa wannan yunkuri da shugaban na Kenya wanda za a iya cewa ba saban ba, to sai dai duk da haka wani bangare na al'ummar kasar Kenya na ganin cewa wannan cin zarafin kasar ne da ma 'yan kasar kazalika hakan zai iya shafar mutuncin shugaban.

Yayin da al'ummar Kenya ke tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu, a hannu guda masana harkokin shari'a na ba su amince da kotun ba domin kuwa kamar an girka ta ne da nufin gurfanar da 'yan Afirka.

Kenia William Samoei Ruto
Mukaddashin shugaban Kenya William Samoei RutoHoto: AP

Gabannin barin shugaba Kenyatta zuwa kotun ta ICC dai ya mika ragamar shugabancin kasar ga mataimakinsa William Ruto bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar, wanda kuma shi kansa Mr. Ruto din na fuskantar tuhuma daga wannan kotu ta kasa da kasa kan cin zarafin Bil-Adama, inda a ranar 10 ga watan Satumba da ya gabata ne ma aka bude sauron sa a wannan kotu.