1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Hari a cibiyoyin lafiya ya karu

Yusuf Bala Nayaya
May 25, 2017

Babban sakataren MDD Antonio Guterres a ranar Alhamis din nan ya yi gargadin cewa wuraren kula da lafiya kamar asibitoci na fama da kai hare-hare a yankunan da ake fadace-fadace a duniya.

https://p.dw.com/p/2da7Z
Antonio Guterres in Kenia
Hoto: Reuters/T.Mukoya

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kira bangarori da ke musayar wuta da juna da su guji kai hare-hare kan fararen hula.

Guterres ya bayyana haka ne a lokacin bude wani taro na Kwamitin Sulhu na MDD mai buri na neman kare fararen hula a lokutan yaki. Da ya bada misali da Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce akwai hare-hare kan asibitoci da likitoci da motocin daukar marasa lafiya a kusan kasashe 20 da ake fama da rikice-rikice a shekarar bara.

Ya ce irin wadannan hare-hare sun fi yawa a kasashen Siriya da Afghanistan inda ake kai hari a wuraren kula da lafiyar da ke zama tudun mun tsira. A cewar likitoci masu kare hakkin bani Adama a Siriya an kai hari sau 400 kan wuraren kula da lafiya tun bayan fadawar kasar rikici a 2011.