1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Matsaloli sun dabaibaye duniya

October 14, 2016

Mambobi na taron Majalisar Dinkun Duniya 193 suka amince jami'in diplomasiyar ya fara aiki daga ranar daya ga watan Janairu dan maye Ban Ki-moon.

https://p.dw.com/p/2RDFR
Schweiz Genf Antonio Guterres
Guterres ya kasance shugaban sashin kula da 'yan gudun hijira a MDD tun kafin wannan lokaciHoto: picture-alliance/dpa/S. Di Nolfi

Bayan da taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da zabin Antonio Guterres a matsayin sabon babban sakataren MDD ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru wajen samar da sauyi a harkokin da ke zame wa duniya alakakai inda ya ce zai yi aiki bisa gaskiya da adalci.

Baki dai ya zo daya awajen zabin tsohon Firaministan Portugal Guterres inda mambobi na majalisar 193 suka amince jami'in diplomasiyar ya fara aiki daga ranar daya ga watan Janairu mai zuwa. Bayan da Ban Ki-moon ya kammala wa'adinsa na biyu a jan ragamar majalisar.

Guterres dai ya ce halin da duniya ta tsinci kanta a yanzu na bukatar duba na nutsuwa wajen tunkarar kalubale- iri-iri da suka yi wa duniyar daurin gwarmai.