1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya yaba shari'ar 'yan Boko Haram a Najeriya

January 9, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa Najeriya kan yadda ake shari'ar mayakan Boko Haram da ake tsare da su da kuma yadda ake kare hakkin bil Adama

https://p.dw.com/p/2qaY3
Den Haag Schlusszeremonie des UN-Kriegsverbrechertribunals für Ex-Jugoslawien | UN-GeneralSekretär Antonio Guterres
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuteresHoto: Reuters/United Photos/T. Kluiters

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wanda ya sanar da wannan yabo a wani rahoto da majalisar ta fitar kan ayyukanta a kasashen Afirka ta yamma ya nemi gwamnati da ma'aikatar shari'a da jami'an tsaro su tashi tsayin daka wajen ganin ana bin dokoki da yarjeniyoyi na kasa da kasa da suka shafi kare hakkin bil Adama.


A zangon karshe na shekarar 2017 ne dai gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutane 1600 da ake zargi mayakan Boko Haram ne a wata shari'a da aka yi a asirce a wasu cibiyoyin tsaro inda aka yanke wa da dama daga cikinsu hukunci bayan samun su da laifi. Haka kuma yayin da shekarar ke karewa rundunar sojin Najeriya ta yanke wa wasu sojojin hukunci saboda samun su da laifin keta hakkin bani Adama matakin da ake gani ya gyara irin kallon da a baya ake yiwa Sojojin na cin zarafin jama‘a ba tare da fuskantar shari'a ba.

Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da manyan jami'an sojiHoto: NPR


Sai dai wasu masu kare hakkin bil Adama kamar Barista Atiku Isma'il wani mai rajin kare hakkin dan Adama a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya na ganin majalisar ta yi gaggawarar yabo. Amma ga masu fashin baki kan harkokin yau da kullum, matakai da ake dauka na yi wa wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne Shari'a abin a yaba ne kasancewar a baya ba a samu hakan ba.

Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Babban hafsan sojin Najeriya da kwamandan rundunar yaki da Boko HaramHoto: Getty Images/AFP

Wannan yabo da Majaliar Dinkin Duniya ta yi wa mahukuntan Najeriyar dai na zuwa a dai-dai lokacin ake shirin gurfanar da wasu sabbin wadanda ake tuhuma da kasancewa 'yan Boko Haram da kuma ci gaba da shari'ar wadanda ba kammala shari'ar su ba a baya.


Jami'in Shari'a na rundunar matasan Civilian JTF Barista Jibril Gunda ya tabbatar da cewa gwamnati ta tanadi isassun lauyoyi da za su bada kariya ga duk wani dan Boko Haram da bai samu lauyan da zai kare shi a shari'ar ba.