1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar zaben Najeriya 2019

Abdullahi Tanko Bala
February 21, 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da babban mai kalubalantarsa Atiku Abubakar sun yi kira ga jama'a su bada hadin kai domin gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali

https://p.dw.com/p/3Dn71
Vor Wahlen in Nigeria  Muhamadu Buhari (M), Präsident von Nigeria, und Atiku Abubakar (r)
Hoto: picture-alliance/AP/B. Curtis

Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce shirya tsaf domin gudanar da zabe a wannan asabar din 23 ga watan Fabrairu 2019.

A makon da ya gabata ne dai hukumar ta INEC ta dage zaben bisa dalilai na matsalar rashin isar kayan zabe a wasu yankunan kasar.

Shugaban kasar Muhammadu BUhari da ke neman wa'adi na biyu da kuma babban mai kalubalantarsa Atiku Abubakar kowannensu ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar mafi girma a Afirka.