1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin ƙawance a Isra´ila

March 24, 2009

Firayi Ministan Israila mai jiran gado Benjamin Netanyahu ya sami nasarar shawo kan shugaban Jamiyyar Labour Ehud Barak wajen ƙulla ƙawancen siyasa

https://p.dw.com/p/HIz1
Shugaban jam´iyar Likud a Isra´ila, Benjamin NetanyahuHoto: AP

Ƙarƙashin wannan ƙawance dai Gwamnatin Netanyahu bisa jagorancin Jam,iyyar Likud, za ta mutunta dukkan yarjeniyoyin ƙasa da ƙasa da Isar'ilan ke ɗamfare a kai, ciki kuwa har da batun tabbatar da 'yantacciyar ƙasar Palasɗinu, inji Shalom Simchom wani mai shiga tsakani daga Jam'iyyar Labour.

Natenyahu wanda zancen nan da ake yi, ya ke ƙoƙarin kaucewa daga maida hankali kan batutuwan wanzuwar lafiya a ɗaukacin iyakokin Isra,ila zuwa batutuwan tattalin arziƙi, ya na kuma sassarfa wajen miƙa goyon baya ga kafuwar ƙasashen biyu, al'amarin da Amurka ta runguma a matsayin mafitar wannan rikici.

A halin da ake ciki yanzu Jagororin Jamiyyar Labour ta Ehud Barak sun rattaba hannu kan daftarin ƙawancen a birnin Tel Aviv. Barak dai wanda alamu suka nuna zai iya cigaba da riƙe matsayin sa na ministan tsaro, na fuskantar adawar gaske daga jam'iyyar sa game da wannan yunƙuri.

Jayayya da batun tabbatuwar ƙasar Palasɗinu da kuma kafa gwamnati ba tare da tsunduma hannan Jam'iyyar Labour ba, zai iya jefa Netanyahu cikin halin fito na fito da Shugaban Amurka Barack Obama, mutumin da ya lashi takobin samar da zaman lafiyar Isra'ila da kuma Palasɗinu.

Game da wannan ƙawance dai, Isaac Herzog, wani minista ɗan Jam'iyyar Labour, cewa ya yi Netanyahu na bin dukkan wasu hanyoyi na nuna sauya alƙibla daga ƙin jinin 'yantacciyar ƙasar Palasɗin. Hakan ce ma ta sanya Netanyahun ke son tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da Yehud Barak mutumin da aka san na goyon bayan kafa 'yantacciyar ƙasar Palasɗinu a yankin kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

Da taimakon wannan ƙawance na Jam'iyyar labour dai, Netanyahu zai sami rinjayen wakilan majalisar dokoki 66 daga cikin su 120, giɓin da yake da damar cikewa kafin cikar wa'adin kafa Gwamnatin Sa, nan da ranar 3 ga watan gobe na Afrilu, sakamakon Zaɓen da aka gudanar a Isra'ilan ranar 10 ga watan fabrairun da ya gabata.

Wata sanarwa daga ofishin Jam'iyyar Likud ta Netanyahu, ta bayyana cewar ƙawancen da aka ƙullawa tsakanin Jamiyyar Labour da ta Likud dai ya haɗar da samar da fahimtar juna ta fuskar tattalin arziƙi da kuma Diplomasiyya.

Mawallafi: Adamu Dabo

Edita: Mohammad Nasiru Awal