1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin hadaka ta Hamas da Fatah

May 29, 2014

Bayan tsawon lokaci suna kai ruwa rana, kungiyoyin Hamas da Fatah na Falasdinu sun bayyana sunan mutumin da zai kasance firaministan gwamnatin da suka amince su girka.

https://p.dw.com/p/1C984
Mahmud Abbas da Rami Hamdallah
Mahmud Abbas da Rami HamdallahHoto: Reuters

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana sunan Rami Hamdallah a matsayin wanda zai kasance firaministan gwamnatin hadakar da Hamas da Fatah suka amince su girka.

Bayan da ya mika masa takarda ta kama aiki, shugaban na Falasdinu ya nemi Mr. Hamdallah ya girka gwamnati sai dai ya zuwa yanzu ba a kai ga yin hakan ba saboda rashin fahimtar juna da aka samu kan wanda za a nada matsayin ministan harkokin waje, ko da dai wata majiya daga ofishin Mr. Abbas na cewar wannan matsala ta kau.

Nan gaba ne dai ake sa ran fidda jerin ministocin da za su yi aiki a wannan gwamnatin ta hadaka wadda kungiyoyin na Fatah da Hamas suka amince da girkawa a makonnin da suka gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar