1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Jamus ta cimma daidaito a kan wasu muhimman batutuwa

November 5, 2012

Bayan wata tattaunawa ta tsawon sa'o'i takwas gwamnatin ƙawance ta amince da soke kuɗin ganin likita da kyautata wa 'yan fansho masu ƙaramin albashi.

https://p.dw.com/p/16czI
Hoto: Reuters

Shekara guda gabanin zaɓen 'yan majalisar dokokin tarayya a Jamus, gwamnatin ƙawancen ƙasar ta CDU/CSU da FDP ta magance taƙaddamar da suke a kan wasu muhimman batutuwa. Bayan sun shafe tsawon sa'o'i takwas suna tattaunawa, wakilan gwamnatin sun amince a farkon shekara mai kamawa za a soke kuɗin da mutane ke biya idan sun je ganin likita wato Euro 10 a kowane rubu'in shekara. Hakzalika sun share fagen ba da kuɗin kula da yara. Jam'iyar FDP ta yi nasara a bukatar da ta gabatar cewa ana iya biyan wannan kuɗi a cikin wata ajiyar banki da daga baya za a iya amfani da shi wajen biyan kuɗin jami'a ko koyan sana'a. A matakin magance talauci a tsakanin tsofaffi, 'yan siyasar na gwamnatin ƙawance sun amince da kyautatawa 'yan fansho masu ƙaramin albashi da kuɗaɗen haraji. 'Yan adawa na jam'iyar SPD sun yi suka ga wannan ƙudurin da cewa wani nauyi ne za a ɗora wa masu biyan haraji.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas