1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta damu da karuwar hare-hare

June 28, 2017

A martaninta na farko bayan sace ‘yan sanda mata kusan 16 da bai wa mutane wa'adin barin garuruwansu a jihar Borno, gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa kan lalacewar lamura a yankin arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/2faMS
Tschad Boko Haram greift Ngouboua an
Jama'a da ke kaurace garuruwansu a jihar BornoHoto: Reuters/M. Nako

Wani kwanton bauna dan 'yan kungiyar Boko Haram suka yi ya sanya su samun damar sace ‘yan sanda mata tsakanin 12 zuwa 16  da ke kan hanyarsa ta rakiyar gawa zuwa jihar Adamawa.Tuni da shugaban Boko Haram din ya bayyana a wani faifan bidiyo da da ya fidda cewar su ne suka kama matan sannan ya sha alwashin kaisu gidan bauta ba tare da bata lokaci ba. Abun kuma da a halin yanzu ke kara tayar da hankali da damuwa ga gwamnatin kasar da a baya ta kalli nasara a cikin yakin amma kuma ke fuskantar gagarumin koma baya a yanzu. Malam Garba Shehu, shi ne kakakin gwamnatin ta Abuja da kuma ya ce gwamnatin za ta yi iyakacin kokari da nufin ceto ‘yan sandan mata da ma ragowar ‘yan kasar  da ke a hannu na kungiyar a halin yanzu.

Walter Samuel Nkanu Onnoghen Chief Justiz für Nigeria
Mahukunta a NajeriyaHoto: Ubale Musa

To sai dai koma ina tarukan gwamnatin ta Abuja ke kaiwa da nufin tunkarar ta'azzarar aiyyukan kungiyar a cikin yankin dai akwai alamun sake karfi na kungiyar da ake da tunanin ta kai ga karba na kudin fansa na ‘yan mata Chibok domin karin karfi da kokari na farfadowa daga dogon suman da sojan kasar suka yi nasarar jefata. Ya zuwa yanzu dai ta kai har ga tunanin gini na shingen kariya a jami'ar Maiduguri da nufin kare kai daga karuwar harin ‘ya' yan kungiyar da ke dada kamari.

Nigeria Armee Anschlag in Abuja 25.6.2014
Dakarun gwamnatin NajeriyaHoto: REUTERS

Yawan ‘yan sanda da sojan da ke aiki a kasar dai a fadar kakaki na gwamnatin ba za su iya kaiwa ga tabbatar da tsaro kan kowa ba, abin kuma da ya ce ya sanya hada hannu da jami'an tsaro zama na wajibi da nufin iya kaiwa ya zuwa karshen matsalar. Ana dai kallon matsalar kishi a tsakanin jami'an tsaron a matsayin ummul aba'isin sake lalacewar lamura a cikin yankin da a baya ya ke fatan maida ‘yan gudun hijira ya zuwa gidaje sakamakon zaman lafiyar da ya samu a bayan.