1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya yi alkawarin cika alkawura

March 1, 2019

Wani taron majalisar zartarwa ta Najeriya ta kare tare da shugaban kasar Muhammadu Buhari yana fadin shekaru hudun da ke tafe za su zamo mai tsauri ga majalisar.

https://p.dw.com/p/3EKgD
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Duk da cewar dai sun je a cikin sunan murna kuma har sun kai ga yabon nasarar tasa dai shugaban kasar bai boye ba ga irin  jan aikin dake gaban ministoci na gwamnatin.

Muhammadu Buhari dai ya shaida wa ministocinsa cewar fa shekaru hudun da ke tafe za su kasance mai zafi ga jami’an na gwamnatin da ya ce sai sun kai ga gaci a bisa alkawuran da ke tsakani da al’umma ta kasar.

Duk da cewar dai Abujar ta ce tana shirin dorawa a bisa muhimman batutuwa guda uku na yakin hanci, da tsaro da ma samar da ayyukan yi a tsakanin al’umma.

Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

Harkar noma dai na zaman ta kan gaba a cikin zuciya ta gwamnatin Najeriya kuma a fadar Engineer Sulaiman Adamu noman rani na shirin ganin daban tun daga shekarar bana.

Ya zuwa yanzu dai batun sulhu tsakani na zaman na kan gaba a cikin tarrayar najeriya bayan wani taron kwamitin tsaron da bangarorin zaben a jiya.

Kuma a fadar sakataren gwamnatin Najeriyar Boss Mustapha gwamnatin kasar tana shirye da karbar sharuda na adawa in har suna da burin biya bukatu na kasa.

Wasu dai a ciki na bukatun a fadar majiyoyi na sakin duk kammamu na siyasa na kasar sannan kuma da cire  takunkumi a kan kowane asusun ajiya na 'yan kasar da gwamnatin kasar ta yi ya zuwa yanzu.