1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nijar ta amince da taron Congres na jam'iyyar CDS Rahama

Gazali Abdu TasawaSeptember 26, 2014

Ofishin ministan cikin gida da ke kula da jam'iyyun siyasa a Nijar ya tabbatar da halalcin sakamakon babban taron CDS wanda ya zabi Alhaji Abdu Labo a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa.

https://p.dw.com/p/1DLny
Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Tuni dai sabbin shugabannin jam'iyyar ta CDS Rahama suka yi tayin sulhu da neman hadin kai ga sauran 'ya'yan jam'iyyar da ke hamayya da su. Sai dai kuma tuni bangaran Alhaji Mahamane Ousman din ya yi watsi da matakin ministan cikin gidan
kasar ta Nijar na amincewa da sakamakon babban taron Congres din jam'iyyar da ma kuma tayin sulhun da sabbin shugabannin jam'iyyar suka yi masu.


A cikin wata wasika ce mai lamba 3004 ta ranar 23 ga watan Satumba ministan cikin gidan na Nijar Malam Hasumi Masa'udu ya tabbatar da amincewarsa da sakamakon taron na jam'iyyar ta CDS Rahama wanda ya wakana daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Satumba na shekara ta 2014 a birnin Yamai.

Shugabancin CDS ya koma hannun Abdu Labo

A wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Jumma'a mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Muntari Kadri ya yi karin bayani a game da ma'anar wasikar
ministan yana mai cewa:

"Gwamnatin Nijar ta yarda da dukka sakamako da muka yanke hukunci a kanshi a wannan zama na Congres. Daga wannan rana shugabancin jam'iyyar CDS Rahama ya koma hannun Abdu Labo, kuma ba wanda zai magana da sunan jam'iyyar bayan Abdu Labo. Kuma duk wanda ya taka doka dole dola za ta hau kansa."

Mahamane Ousman Ex-Präsident Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Taron Congres na jam'iyyar ta CDS Rahama dai ya wakana ba tare da bangaran Alhaji Mahamane Ousman ya halarce shi ba. Kuma tuni ya yi watsi da sakamakon da taron ya cimma a bisa hujjar cewa haramtaccen taro ne da ya saba wa doka.

Shari'a ba ta kare ba, matakin minista bai da tasiri

Kuma da take tsokaci a kan matakin da ministan cikin gida ya dauka a yanzu na amincewa da sakamakon taron jam'iyyar, bangaran Alhaji Mahaman Usmane ta bakin shugaban kungiyar matasan jam'iyyar na kasa Malam Mohamadu Nuridin Musa cewa ya yi "matakin ministan bai da wani tasiri domin bai da hurumin mika wanann jam'iyya ga wani bangare a daidai lokacin da shari'a ba ta kare ba."

To sai dai duk da haka mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Muntari Kadri wanda ke a matsayin shugaba na riko a madadin sabon zababben shugaban jam'iyya Alhaji Abdu Labo da ke tsare a yanzu haka a gidan kurkukun garin Say a kan maganar zargin cinikin jarirrai tayin neman sulhu ya yi ga abokanin hamayyar tasu.


Ko ma dai me ake ciki za a iya cewa yanzu jam'iyyar ta CDS Rahama wacce ta taba shugabancin kasar Nijar da ma haifar da jam'iyyun siyasa kusan 15 daga cikinta a cikin kasa da shekaru 20 sabili da yawan rikicin da ake samu a tsakanin 'ya'yanta, ga bisa dukkan alamu wannan Congres bai sa ta rabu da bukar ba inda yanzu haka ta sake shiga cikin wani yanayi na mai abu ya rantse maras abu ya rantse a daidai lokacin da ya rage kasa da shekara daya da rabi a shiga zabuka a Nijar.