1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara ga dokar yaki da ta'addanci a Kenya

Ahmed SalisuJanuary 2, 2015

Wata kotu a kasar Kenya ta ce ta jingine wasu sassa takwas na sabuwar dokar nan ta yaki da ta'addanci da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a makonnin baya.

https://p.dw.com/p/1EEEu
Kenia Präsident Uhuru Kenyatta in Nairobi
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Mai shari'a George Odunga ya ce kotun ta dau wannan matakin ne domin a ganinta bai kamata a ce an yi amfani da dokar wajen tauye hakkin dan Adam a kasar ba don haka ba za a yi amfani da sassan da aka jingine ba har sai alkalin alkalan kasar ya kafa kwamiti na mutum uku da za su duba ta don tantance sahihancin dokar baki daya.

Daga cikin irin abubuwan da alkalin ya jingine na dokar dai har da sashen nan da ya yi tanadin daurin shekaru uku ga manema labarai a gidan maza in sun watsa labarai da gwamnati ke ganin za su yi nakasu ga bincike da jami'an tsaro ke yi. Tuni dai 'yan jarida da kungiyoyin kare hakkin bani adama a ciki da wajen kasar suka yi na'am da wannan mataki da kotun ta dauka.