1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗarin jirgin NATO a Afganistan

September 21, 2010

Wasu dakarun yamma sun mutu a wani haɗarin jirgin sama da ya auku a Afganistan

https://p.dw.com/p/PII3
Janar David Petraeus,Hoto: AP

Ƙungiyar tsaro ta NATO ta ba da rahoton cewa wani haɗarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya faru a kudancin ƙasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar sojojinta tara, tana mai cewa babu wani abu da ya nuna cewa harbo wannan jirgi aka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa haɗari shi ya kawo yawan sojojin ƙawancen da suka mutu a bana zuwa 529, wanda haka ya kuma nuna cewa shekara ta 2010 ita ce shekarar da aka fi samun yawan mace macen sojojin, tun bayan lokacin da Amirka ta jagoranci yaƙi don murƙushe 'yan ƙungiyar Taliban a shekara ta 2001.

Ko da yake Kungiyar ta Nato ba ta bayyana kasashen sojojin da suka mutu a wannan haɗari ba, amma tace akwai wasu mutane uku a cikin jirgin da ba su mutu ba amma sun samu raunuka. An bayyana ɗaya daga cikinsu ɗan ƙungiyar ƙawancen sojojin ne, ɗaya sojan Afghanistan ɗaya kuma Ba'amurke ne farar hula.

Mawallafiya: Halima Umar Sani

Edita: Umaru Aliyu

.