Haɗin kan ƙungiyoyin AU da EU
November 21, 2013Ƙungiyar Gamayyar ƙasashen Afirka, da Ƙungiyar Tarayyar Turai sun gudanar da tattaunawarsu ta shekara-shekara a birnin Brussels, inda sukan duba batutuwan da suka shafi hakkin bil adama a nahiyoyin biyu. A wannan karon sun gano cewa duk da ci-gaban da ake samu a wasu mahimman fannoni har yanzu akwai ƙalubale, musamman a Turai, inda ake zargin rashin mutunta hakkokin masu gudun hijira da masu neman mafaka ta siyasa.
Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, wadda ita ma ta kasance a taron, ta nuna damuwarta dangane da rashin mutunta masu fafutukar kare hakkin jama'a a nahiyar Afirka, da take hakkokin jama'a da hana wa jama'a walwalar tarayya ko kuma ma'ammala da waɗanda suke so su yi, A Turai kuma mutunta hakkokin masu gudun hijira.
Matsalolin kare hakkin bil adama a Turai
Ko da shi ke, tun kafin gudanar da taron nasu, aka gudanar da wata zama ta fararen hula wanda ya dadale wasu mahimman matsaloli kamar yadda darektan ƙungiyar kare haƙƙin bil adama na shiyar Afirka, Baniel Bekele ya bayyana:
"A tattaunawar da fararen hula suka yi kafin zaman ƙungiyoyin biyu, sun nuna damuwa kan rashin mutunta hakkin ɗan adam, da ma irin barazana da cin zarafin da masu fafutukan kare hakkin ɗan adam, 'yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula ke fuskanta, da ma yadda amfani da dokokin ƙasa da manufofi wajen musgunawa jama'a ke ƙaruwa, wanda kuma ke hana fararen hula gudanar da ayyukansu yadda ya kamata"
Dangane da yadda matsalar ta shafi Turan kuwa, ƙungiyoyin fararen hulan sun yi kira ga majalisun zartarwar ƙungiyoyin da su samar da manufofin da zasu yi la'akari da hakkin bil adama.
Musgunawa 'yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula
Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin na AU da EU da su mayar da hankali wajen shawo kan matsalolin da kafofin yaɗa labarai ke fuskanta daga ƙasashen su Darektan ƙungiyar a yankin Afirka, Daniel Bekele ya yi ƙarin haske:
"Batu ne mai sarƙaƙiya, kuma ba wannan ne karon farko da ake tayar da wannan batu, kuma matakin da ya dace a ɗauka shi ne kwaskware wasu daga cikin dokokin dake da tsaurin gaske, waɗanda ke takurawa kafofin yaɗ labarai masu zaman kansu a Turai da Afirka, musamman ma a Afirka, saboda ƙaruwar da muke gani a Afirka, kwanan nan ne muka ga inda gwamnatoci suka fara amfani da dokokin dake hana kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu da ƙungiyoyin fararen hula gudanar da ayyukansu yadda ya kamata."
Manufofin ƙasashen Turai masu tsauri
Yawancin waɗanda ke gudun hijira suna guduwa ne daga ƙasashen da ke fama da gwamnatoci masu mulkin danniya, kuma har wa yau wasunsu mutane ne da ke fiskantar barazana daga mahukuntan ƙasar, to ko ta yaya ƙungiyar kare haƙƙin bil adaman ke ganin cewa ƙungiyar ta EU zata taimaka wajen ganin cewa an ɗauki masu gudun hijira.
"Manufofin turai kan gudun hijira musamman kan iyakokinta, sun mayar da hankali ne kan tasa ƙeyar 'yan gudun hijira da fararen hula, maimakon ceton rayukan mutane musamman kan teku, saboda haka mun yi kira ga ƙasashen Turai da su ba da mahimmanci wajen mutunta rayukan jama'a a maimakon ɗaukaka dokar su ta kula da kan iyaka, su ceto mutanen da suka sami kansu cikin mawuyacin hali, domin ganin an kai su ƙasar Turan da ya fi kusa da inda suke a ba su matsugunni maimakon sanya fifiƙo kan tsaron kan iyaka.A ƙarshe dai ƙungiyoyin sun cimma matsayar ɗaukar matakan da zasu taimaka wajen samar da cigaba mai ma'ana.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane