1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hada karfi waje guda a yaki da Ebola

November 6, 2014

Kungiyar Tarayyar Turai da kuma kamfanonin harhada magunguna sun ce za su ci gaba da taimakawa tukuru wajen yakar Ebola.

https://p.dw.com/p/1DiZH
Hoto: picture-alliance/dpa/Kristin Palitza

Kungiyar ta EU dai da kafanonin hada magungunan sun ce za su zuwaba kudi Euro miliyan 280 kwatankwacin dalar Amirka miliyan 350 domin gudanar da bincike a kan cutar Ebola mai saurin kisa, inda mafi yawan kudin za a yi amfani da shi ne wajen samar da injinan gwaje-gwaje da kuma alluran rigakafin cutar. Tallafin kudin za a yi amfani da shi ne karkashin shirin samar da magunguna na Innovative Medicines Initiative (IMI) da hukumar kungiyar Tarayyar Turai da kuma kamfanonin harhada magunguna ke daukar nauyinsa. Kawo yanzu dai annobar cutar ta Ebola da ta balle a yankin yammacin Afirka ta hallaka kusan mutane 5,000.

Mawallafiya:

Edita: